Ba zan koma APC ba – Ortom
Tsohon gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya karyata rahotannin sauya shekar sa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Da yake magana a wajen fadada taron zartaswar jam’iyyar PDP, a ranar Litinin, Ortom ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar ne.
KARANTA WANNAN LABARIN:Faduwar Naira: Ka yi tunanin dawo da tallafin man fetur – Kira ga Tinubu
A cewar Ortom: “Rade-radin cewa zan sauya sheka zuwa APC, ba zan je ko’ina ba; wannan da suke kirana da shugaban jam’iyyar a jihar mai dimbin nauyi, ba zan bar wa kowa ba.
“APC ba ta gayyace ni ba. Ni ba mai shagaltuwa ba ne da za a yi hijira daga wannan wuri zuwa wancan, na jajirce zuwa jam’iyya ta (PDP). Wajibi ne mu mutunta jam’iyya a kowane lokaci. Mu yi dabarar komawa mulki. Yanzu ne lokacin da za mu tsara, dole ne mu tsara gaba da su kamar yadda suka yi a 2023. ”
Ortom ya kuma yi watsi da ikirarin samun sabani da tsohon gwamna Gabriel Suswam da Sanata Abba Moro.
“PDP ce kawai jam’iyyar da ke da karfi da kuma karbuwar bukatun jama’a. Da sabon alkawarin da muka yi, za mu sa jam’iyyar ta kara zage damtse a gobe.
“Za mu yi nasara a zabuka masu zuwa. Ba ni da wani sabani da Moro da Suswam, ”in ji shi
A wani labarin kuma:JAMB ta fara rajistar masu son karatu kai tsaye
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta fara sayar da fom na masu son shiga jami’a kai tsaye, DE, a duk fadin kasar nan da kuma wasu zababbun cibiyoyi na kasashen waje.
Kakakin hukumar, Fabian Benjamin ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.