Babban Hafsan Tsaro ya ba da umarnin ida kakkabe ƴan Boko Haram da ISWAP baki daya
A ranar Alhamis ne babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya ziyarci dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK).
Irabor ya yabawa irin rawar da suke takawa tare da tuhume su da su kawar da sauran masu tada kayar baya da ke ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Legas ta Gurfanar Da Makarantar Chrisland, Da ma’aikata Hudu
Babban hafsan sojin ya yi wa sojojin jawabi ne a ofishin a ɗakin taro da ke Maimalari Cantonment a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
“Tabbatar da cewa an kama ‘yan ta’addar Boko Haram da Islamic State West Africa Province (ISWAP) daga maboyarsu,” inji shi.
Hukumar ta CDS ta lura da cewa akwai ragowar kungiyoyin ta’addanci da ke tsugune a cikin dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi.
Irabor ya ce ana samun gagarumin ci gaba a ayyukan hadin gwiwa na sojoji domin dawo da zaman lafiya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.
A halin da ake ciki sojojin bataliya ta 222 sun yi nasarar dakile wani farmaki da mayakan ISWAP suka kai musu a kauyen Ajiri dake karamar hukumar Mafa.
Harin da Abou Muhammed ya jagoranta ya biyo bayan kashe ‘yan ta’adda 41 da kwamanda Abu Zahra, bayan da dakarun gwamnati suka kai samame a kauyukan Mukdolo da Kashi, a karkashin karamar hukumar Dikwa, a ranar 26 ga Maris.
A wani labarin kuma:Ba Da Niyya Na Cakawa Budurwata Wuka Ba – Dan China Ya Fadawa Kotu
Wani dan kasar China, Mista Frank Geng-Quangrong, mai shekaru 47 a ranar Alhamis ya shaida wa wata babbar kotu aKano cewa ya daba wa budurwarsa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani ‘yar shekara 22 da haihuwa wuka ba da niyya ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake tuhuma, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, yana fuskantar shari’a kan laifin kisan kai.