A ranar Talata ne babban hafsan hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa, ya ziyarci wadanda suka jikkata a Sokoto tare da zaburar da sojoji domin kara kaimi a wani bangare na bukukuwan Kirsimeti.
Musa ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai don yakar abokan gaba na kasar domin marawa rundunar sojin Najeriya baya domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara lami lafiya.
Karanta nanDole Ne Mu Hada Kai Don Tabbatar Da Zaman Lafiya a Najeriya — Tinubu Ga gwamnoni
Ya je Sokoto ne domin yin mu’amala da ma’aikatan da suka jikkata da sauran wadanda ke gudanar da ayyukansu a fagagen aiki daban-daban a yankin.
A cewar sa, wannan lokacin ya kasance lokacin biki da annashuwa kuma rundunar sojin Najeriya ta ga ya dace a yi bikin tare da dukkan jami’an tsaro tare da yi wa wadanda suka sadaukar da kai addu’a.
Musa ya yi kira ga wadanda suka samu raunuka da su dauki lamarin a matsayin kaddara, yana mai ba da tabbacin cewa sojojin Najeriya na tare da su gaba daya kuma za su ci gaba da ba su goyon baya don samun sauki da komawa bakin aiki.
A wani labarin kumaFilato: Kakakin Majalisa Abbas Ya Yi Allah-Wadai da Sabbin Kashe-Kashen Da Aka Yi
Ya kuma mika godiyarsa ga sojojin da ‘yan Nijeriya bisa jajircewar da suke yi, ya kuma kara da cewa ya kamata a amince da sadaukarwar da duk jaruman da suke sanye da rigar kare kasa suka bayar.
Ina ba ku kwarin gwiwar fuskantar kalubalen tare da hadin kai da jajircewa, jarumtar ku ba za ta wuce gona da iri ba, kuma mun yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya.