Babban Limamin Suleja Ya Rasu, Sa’o’i Bayan Dawowa Daga Aikin Hajji
Babban Limamin Babban Masallacin Suleja da ke Jihar Neja, Sheikh Dahiru Shuaibu, ya rasu ne a ranar Asabar din nan sa’o’i kadan bayan ya dawo daga aikin hajji a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Wani daga iyalan mai suna Abduljalil Dahiru Shuaibu ya ce limamin da ya dawo daga Saudiyya a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 9 na safe ya rasu ne sakamakon bugun zuciya da ya yi da misalin karfe 11 na dare a gidansa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda Yan Sanda Suka Harbe Wani Dan Acaba Dan Arewa A Legas
Ya ce, “Ina cikin ’yan uwa da suka je filin jirgin saman Abuja da safiyar Asabar don tarbar limamin da ya dawo gida. Amma da misalin karfe 11:00 na dare, sai aka yi min waya cewa liman ya rasu.”
City & Crime ta samu labarin cewa limamin wanda ya rasu yana da shekaru 76, Khadi ne mai ritaya a kotun daukaka kara ta Shari’a da ke Minna a Jihar Neja, kuma ya auri mata hudu, yana da ‘ya’ya 30 da jikoki da dama.
City & Crime ta ruwaito cewa an binne gawarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a makabartar Musulmi ta Suleja.
A wani labarin kuma:Yadda Daliban Wata Makarantar Sakandire Suka Lakadawa Malamin Su Duka
Wani gungun dalibai na makarantar sakandire su 10 a jihar Ogun sun yi wa wani malami mai suna Kolawole Shonuga duka, wanda ya hana daya daga cikin su sata a lokacin jarrabawa.
City & Crime ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata a Isanbi Comprehensive High School, Ilisan-Remo, karamar hukumar Ikenne.