A ci gaba da kokarin rage cinkoso a gidajen gyaran hali, babban alkalin jihar Ogun, Mai shari’a Mosunmola Dipeolu ya yi wa fursunoni 20 afuwa a sassan kananan hukumomin uku na jihar.
Da yake jawabi a dakin taro na rukunin ma’aikatan shari’a da ke Abeokuta, a yayin sakin fursunonin, Mai shari’a Dipeolu ya ce an sallami goma a Abeokuta, biyu daga Ijebu-Ode, bakwai daga Ilaro, daya kuma daga gidan gyarane Hali na Sagamu
Babban Alkaliyar ta bayyana cewa wadanda aka yi wa afuwar sun kasance a tsare na tsawon wasu shekaru da laifuffuka daban-daban da suka hada da fyade, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu, inda ya shawarce su da kada su koma cikin aikata laifuka.
“Mutane na ci gaba da shigar da kara kamar yadda suka san hakkinsu, shi ya sa muke ci gaba da kara adadin alkalai gwargwadon yadda gwamnati za ta iya. Har ila yau, muna ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a don sanin hakkinsu, saboda jinkirin da ake yi na adalci ba shine abin da muke so a jihar ba,” inji ta.
Ta bayyana cewa an gudanar da atisayen ne a babban kotun jihar, maimakon ziyarar da aka saba kai wa a cibiyoyin gyaran hali a jihar sakamakon annobar COVID-19, inda ta yi alkawarin cewa za a sake yin wani bangare na sakin Wasu Fursunoni nan da watanni hudu masu zuwa.
A nasa bangaren, Kwanturolan gidan gyaran hali na jihar, Alimi Rasheed, ya ce gwamnatin tarayya ta kara zage damtse wajen kula da rage cinkoso a gidajen gyaran hali a jihar, yana mai godiya ga gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta bayar wajen ganin an tabbatar da adalci cikin gaggawa.