Enemi George, daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da suka koma jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya ce ba zai koma jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, tsohuwar jam’iyyarsa ba.
George ya bayyana cewa 27 daga cikin su da suka koma APC sun jajirce wajen goyon bayan shirin ‘Renewed Hope Agenda’ na Shugaba Bola Tinubu.
Karanta nanGobara Ta Lakume Dukiyar Naira Miliyan 300 A Anambra
Ya yi magana ne a ranar Laraba yayin da yake gabatar da tambayoyi a matsayin bako a shirin Siyasar Yau na Channels Television.
Mun koma APC domin mun zabi shugaban kasa, idan muka ga Mr President ya cancanci kuri’unmu to ina ganin ya dace mu goyi bayansa.
Mun koma don shiga ajandar sa ta Renewed Hope don yin aiki tare don tabbatar da cewa abin da ‘yan Najeriya ke bukata sun samu in ji George.
Jahar Ribas dai ta tsunduma cikin rikicin siyasa sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa Nyesom Wike.
Lamarin dai ya janyo rarrabuwar kawuna a majalisar, inda 27 daga cikinsu suka fice daga PDP zuwa APC mai mulki.
A wani labarin kumaAn Kama Mutane 5 Da Suka Mallaki Bindiga Ba Bisa Kaida Ba A Katsina
Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutane biyar da aka samu da mallakar bindiga kirar AK-47 ba bisa ka’ida ba a kauyen Kurmi da ke karamar hukumar Bakori.
ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, kakakin rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a Katsina.
A ranar 19 ga watan Disamba, 2023, bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an mu da ke hedikwatar ‘yan sanda reshen Bakori, tare da hadin gwiwar ‘yan banga a lokacin da suke sintiri, sun yi nasarar gano tare da kama mutane biyar.