Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya soki hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke na soke nasarar Gwamna Abba Yusuf.
Lauyan kare hakkin dan Adam ya yi magana a gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda ya dage cewa watsi da kuri’u 165,000 kan rashin yin tambari bai dace ba. Ya ce bai kamata alkalai su hukunta masu kada kuri’a kan kura-kuran da INEC ta yi ba.
Karanta nanIna Tausaya Wa ‘Yan Nijeriya Da Basuda Kudin Fita Kasashen Waje-Bishop Kukah
Ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kura-kuran da INEC ta yi ba. Wannan shi ne abin da ya faru kwanan nan a Kano, inda aka ce kuri’u 165,000 da jami’an INEC ba su samu ba,” inji shi.
Falana ya kara da cewa muna rokon alkalan mu da su rungumi adalci—babban adalci—ta hanyar da ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran INEC ba. Ba za ku iya kalubalanci ingancin katunan zabe ba.
Lauyan kare hakkin bil’adama, Mista Femi Falana, SAN, a ranar Juma’a, ya soki hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke wanda ya soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
A wani labarin kumaNayi Asarar Miliyoyi Saboda Bata Min Suna Da Wanda Na Shigar Kara Yayi-Gabon
Ku tuna cewa kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Kano ta soke zaben Gwamna Yusuf.
Sai dai da yake magana a shirin Channels TV Sunrise a ranar Juma’a, Falana ya ce: “Ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran INEC ba. Abin da ya faru kwanan nan kenan a Kano, inda aka ce kuri’u 65,000 da jami’an INEC ba su samu ba.
Muna rokon alkalan mu da su rungumi adalci, adalci mai yawa, ta yadda ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran INEC ba.