Ministan yada labarai da al’adu, Mista Lai Mohammed, ya yi Allah-wadai da sanya Najeriya cikin sunayen da da gwamnatin Burtaniya ta yi na hana su shiga kasar kan sabon nau’in omicron na COVID-19.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, Mista Lai Mohammed ya bayyana matakin a matsayin rashin adalci da nuna wariya.
Ministan ya kuma yi kira ga gwamnatin Burtaniya da t janye matakin da suka dauka cikin gaggawa.
Har ila yau, an tattauna a taron kolin, yadda za a cigaba, dangane da cigaban martanin da ake samu a halin yanzu, game da cutar, da suka hada da cigaba da yin alluran rigakafi, sa ido, da kuma tantancewa a wuraren shiga daban-daban.
Kalaman Lai Mohammed sune martani na baya-bayan nan game da hukuncin na Burtaniya da ke cigaba da janyo cece-kuce a Najeriya da ma duniya baki daya.
Tun da farko, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin Burtaniya ta sanya Najeriya cikin jerin wadan da zata hana shiga kasar ta biyo bayan gano nau’in COVID-19 na Omicron.
“Ba mu yi farin ciki ba lokacin da aka sanya kasashe shida a yankin kudu da hamadar Sahara a cikin jerin wadan da za a hana shiga turai, kuma hukumar ta WHO ta kuma ba da shawarar a guji hana juna tafiye-tafiye,” in ji ministan a gidan talabijin na Channels ta cikin shirin Sunday Politics, kasa da kwana guda bayan Birtaniya ta sanar da daukar matakin.
“Daga abun da muka sani game da COVID-19, akwai hanyoyi da yawa don sarrafa shi, ban da haka, ba a san da yawa game da bambance-bambancen Omicron ba. Mun san, alal misali, cewa ba a sami asarar rayuka ba. Ba a sami rahoton rashin lafiya mai tsanani ba.
Dimokuradiyya ta rawaito ministan na cewar, matakin bai dace ba. Ya kuma kara da cewa hakan zai yi tasiri da yawa kan harkokin kasuwanci, da kuma kawo cikas ga harkokin kasuwanci a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.