Babu wani shiri na haramta kungiyar ASUU a karkashin Gwamnatin Buhari – Ngige
Tsohon ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige ya karyata kalaman da dan majalisar wakilai Aminu Goro ya yi na cewa akwai wani shiri na haramta kungiyar malaman jami’o’i a karkashin tsohuwar gwamnatin shugaban kasa. Muhammadu Buhari.
Ngige, wanda ya rike mukamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi a tsawon shekaru takwas na gwamnatin Buhari ya bayyana kalaman da Goro ya yi a matsayin tarin karya da kage.
KARANTA WANNAN LABARIN:Peter Obi maketaci ne Daya hana Atiku shugabancin Najeriya– Reno Omokri
A jawabin da ya gabatar a zauren majalisar ta 9, dan majalisar ya bayyana yadda kakakin majalisar mai barin gado kuma sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya ceci ASUU daga takurawa gwamnatin Buhari.
Sai dai da yake mayar da martani ta ofishin yada labaran sa, Ngige ya bayyana labarin Goro a matsayin labarin kanzon kurege, inda ya ce babu irin wannan abu da ya faru irin haka a karkashin gwamnatin Buhari.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa ba ya bukatar amincewar shugaban kasa a matsayinsa na ministan kwadago da samar da ayyukan yi don janye takardar shaidar rijistar kungiyar kwadago da ta yi kuskure.
Ya kara da cewa sashe na 7 na dokar kungiyar kwadago ta shekarar 2004, ya baiwa magatakardan kungiyar damar soke takardar sheda, fiye da yadda ASUU ta karya sashe na 37 kan yadda ake karkatar da asusu na shekara-shekara.
A wani Labarin Kuma:Shehu Sani Ya Yi Wani Shagube Mai Zafi Ga El-Rufa’i Na Kin Nada Shi Mukamin SGF Da Tinubu Ya Yi
Dan rajin kare hakkin jama’a kuma tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rifa’i a matsayin wuka mai guba, inda ya ce shugaban kasa Bola Tinubu yayi hikima da Bai nada shi cikin mukarraban sa na kusa-kusa ba.
Sani, wanda ya yi wa tsohon gwamnan Kaduna shagube, ya bayyana shi a matsayin shugaban siyasa mai raba kan jama’a, wanda a kullum yake amfani da banbance-banbancen addini don biyan bukatun kansa.