Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce babu wani shugaban Najeriya da zai iya samar da sabuwar Najeriya cikin tsakar dare.
Obasanjo ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron kasa da kasa kan ‘Zurfafa al’adun dimokuradiyya da cibiyoyi don ci gaba da tsaro a Najeriya’ a Fatakwal a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: ICPC Ta Sake Damke Tsohon Magatakardar JAMB, Ojerinde
A cewar Obasanjo, hawan mukaman siyasa baya baiwa masu rike da madafun iko damar ruguza manufofi da shirye-shiryen magabata.
Tsohon shugaban kasar ya ce duk da cewa ba komai jam’iyyar da ta gabace ta, ya kamata sabbin shugabanni su ci gaba da tsare-tsare da ayyukan magabata kamar yadda shirye-shiryen ke da amfani ga jama’a.
Obasanjo ya ce, “A Najeriya, kowacce sabuwar gwamnati ta kasance tamkar Najeriya sabuwar kasa ce,” in ji shi yayin jawabinsa mai taken, ‘Mutunta Ka’idojin Dimokuradiyya.
“Hakika, a lokacin yakin neman zabe, wasu shugabannin suna jin kamar suna shirin sake farfado da Najeriya da kirkiro sabbin ‘yan Najeriya cikin dare. Wato saboda sun rasa bangaren dimokuradiyya wanda ke jaddada ci gaba, kwanciyar hankali da tsinkaya.
“Gwamnati daya na iya aza harsashi amma tana bukatar gwamnatoci da yawa su ci gaba da ginawa mai inganci a kan harsashin.
“Abin da ya faru ne saboda muna yin watsi da yawancin ka’idojin dimokuradiyya. Kuma ko ta yaya, ba ma jin dadin barnar da muke yi a daidaiku da kuma a dunkule, ga tsarin al’umma,” inji shi.
Obasanjo ya jaddada cewa dimokuradiyya ba abin mamaki ba ne na kwana daya, yana mai cewa dole ne a samu ci gaba da hasashen manufofin duk da sauye-sauyen shugabanci.
A wani labarin kuma,
Dalilin Da Yasa Shugaban Kasa Mai Zuwa Zai Gaza Kamar Jonathan Da Buhari – Farfesa Ibrahim
Wani Farfesa a Kimiyyar Siyasa kuma memba a Hukumar Gudanarwa ta Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba CDD, Jibrin Ibrahim, ya ce akwai yiyuwar shugaban kasar Najeriya na gaba ya gaza kamar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari mai ci.
Da yake jawabi a wajen taron tattaunawa na kafafen yada labarai karo na 20 mai taken, “Tambaya da ajandar shugaban kasa a 2023” da aka yi ranar Alhamis a Abuja,Farfesa Ibrahim ya ce yayin da ‘yan takarar shugaban kasa suka gabatar dalla-dalla kan abubuwan da suke son yi idan aka zabe su, sun gaza don bayyana yadda za su yi.