Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya caccaki tsohon mataimakin gwamnan jihar, Ahmed Mahmoud Gumel kan kalaman da ya yi kan jam’iyyar APC, bayan ficewa daga jam’iyyar.
Gwamna Badaru ya mayar da martani ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a karamar hukumar Birnin-kudu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za mu ci gaba da daukar kwararan matakai don kare mutanenmu – Abiodun
DAILY POST ta ruwaito cewa tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana cewa zaman sa a jam’iyyar APC na cike da kunci da radadin bakin ciki.
Ya ce gwamnatin APC ta kasa cimma buri da muradin talaka, ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ba ta shirya yin nasara a zaben 2023 mai zuwa ba.
Sai dai da yake mayar da martani kan sanarwar, Gwamna Badaru ya ce sun yi addu’ar Allah ya tona asirin masu yiwa jam’iyyar APC zagon kasa.
“Allah Ta’ala ya ci gaba da tona asirin mayaudari, butulci, wadanda suka kasance suna fada da rantsuwa kan karya da farfaganda.
“Wannan mutumin da yake cewa ba mu shirya yin nasara ba, shi ne wanda ba shi da gaskiya, shi ya sa ya yi tsalle ya koma wata jam’iyya,” in ji Badaru.
A wani labarin kuma, Carabao Cup: Jadawalin Matakin Daf Da Na Karshe
A daren Laraba ne aka gudanar da jadawalin wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin Carabao. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Southampton wacce ta doke zakarun gasar Premier Manchester City za ta kara da Newcastle United.