Balaguro: Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Ƙasarta da kada su Ziyarci Jihohi 18 A Najeriya
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shawarci Amurkawa da su sanya lura yayi balaguron zuwa Najeriya “saboda ayyukan ta’addanci da garkuwa da Mutane da sauran ayyukan ƴan bindiga.”
Bayan sabunta shawarwarin tafiye-tafiyen da aka yi a ranar Laraba, Amurka ta lura cewa wasu yankuna “sun kara zama masu haɗari”
Ta shawarci ‘yan kasarta da su guji zuwa Jihohin Borno Yobe Kogi da kuma arewacin Jihar Adamawa saboda ta’addanci da garkuwa da mutane, sai
Bauchi Gombe Kaduna Kano Katsina Sokoto da Zamfara saboda garkuwa da mutane, sai Abia Anambra Bayelsa Delta Enugu Imo da Ribas (ban da cikin Fatakwal) saboda sace-sacen mutane da gungun yan Ta’adda dauke da makamai.
Ya kuma ƙara da cewa “mummunan laifuka – kamar fashi da makami da yin garkuwa da mutane, fashi a gefen hanya da fyade – ya zama ruwan dare a fadin kasar.”
KARANTA NAN:Rashin Tsaro: Gwamnatin Kebbi ta dakatar da haƙar ma’adinai
Ya ƙara da cewa, “Satar mutane domin neman kuɗin fansa na faruwa akai-akai, wanda kwanan nan ma ya faru akan wasu ‘yan kasa biyu da suka dawo Najeriya daga ziyara da kuma wani Ɗan kasar Amurka mai dukiya, kungiyoyin ƴan Ta’addan sun kuma addabi al’umma.
‘Yan ta’adda na ci gaba da shirya makarkashiya da kai hare-hare a Najeriya, ‘yan ta’adda na iya kai hari ba tare da wani gargadi ko kaɗan ba a kai a kai, a kan shaguna a kasuwannin, a otal-otal, a wuraren cin abinci da cibiyoyin Gwamnati, da cibiyoyin sufuri da sauran wuraren da jama’a ke taruwa.
Ƴan Ta’addan kuma suna aiki ne tare da ɓata garin cikin al’umma don cimma burin su.
Akwai tashin hankalin jama’a da gungun ‘yan bindiga a sassan Kudancin Najeriya musamman a yankin Neja Delta da kuma yankin Kudu maso Gabas Masu aikata laifuka da suka hada da sace-sacen jama’a da kai hare-hare kan jami’an tsaron Najeriya, su ma sun zama ruwan dare a wannan yanki.
Rikici na iya barkewa tsakanin al’ummomin manoma da makiyaya a yankunan karkara.
Gwamnatin Amurka tana da iyakacin ikon ba da agajin gaggawa ga ‘yan kasar Amurka a yankuna da dama na Najeriya saboda yanayin tsaro.”
Sai dai ta shawarci ‘yan kasar da har yanzu suka zabi tafiya Najeriya da su “Dauki ingantaccen katin shaida gami da fasfo din Amurka tare da bizar Najeriya na yanzu idan ana bukata.
“Kula da kafofin watsa labarai na gida don samun bayanan abubuwan da ke faruwa, kuma ku kasance cikin shiri don daidaita tsare-tsaren ku,
Ku kula da kewayenku, ku
Kasance a faɗake a wuraren da turawan Yamma ke yawan zuwa,
A guji zanga-zanga da manyan tarukan siyasa,
Yi bitar tsare-tsaren tsaron ku na sirri”, An shawarce su.
Ku yi tsari mai kyau domin ganin ba ku dogara kacokan ga taimakon Gwamnatin Amurka ba, Kafa ƙa’idar “tabbacin rayuwa” tare da Makusantan ku, domin idan an yi garkuwa da ku ƙaunatattunku su san takamaiman waɗanda aka yi garkuwa da su don tabbatar da cewa kun samu ɗauki a lokacin da ya dace.