Wani dan gwagwarmayar ganin Sen Aminu Waziri Tambuwal ya zama sabon shugaban marasa rinjaye a Majalisa ta goma Malam Atiku Muhammad Yabo Sarkin Yakin Yabo
Ya nuna damuwarsa akan wanda shugaban majalisar dattawa Sen Godswill Akpabio ya bayyana a matsayin Sabon shugaban marasa rinjaye a Majalisa ta goma
Inda yace su a ta wajensu ba zasu yarda da abin da ya kira dauki dora ba a majalisa, Atiku Muhammad Yabo ya bayyana matukar bacin ransa akan abinda Akpabio ya yi
KARANTA NANGwamnan Jigawa Namadi Ya Aike Da Jerin Sunayen Kwamishinoni Ga Majalisar Dokokin Jihar
Akpabio dai ya bayyana Sanata daga Jahar Filato Simon Mwadkon a matsayin Sabon shugaban marasa rinjaye abinda bai yima wasu dadi ba
Kamata yayi ace duk wanda zai zama Sabon shugaban marasa rinjaye ya kasance gogagge kuma wanda yasan majalisar kamar Aminu Waziri Tambuwal Inji Sarkin Yaki
To amma da rana tsaka wasu sun dora mana son ra’ayinsu wanda ba shi muke so ba,zanso Akpabio ya amsa min tambayata shin wai shine ya keda alhakin zaben shugaban marasa rinjaye ko kuma Jam’iyar PDP
Idan har bashi da wannan amsar to ya amsa cewar ya yi kuskuren ayyana wani a wannan matsayin na shugaban marasa rinjaye wanda ba Tambuwal ba
Domin shi Tambuwal mutum ne mai kishin kasa kuma wanda ya rike mukamai da dama a matakin Jaha da kuma tarayya
A WANI LABARIN KUMA
Majalisar Wakilai Zata Kafa Tarihi A Karkashin Jagorancin Abbas-Agbesa
Dan Majalisa mai wakiltar Ado Okpokpwu Hon Philip Agbese ya bayyana cewar akwainyiwuwar majalisa ta goma ta kafa wani babban tarihi idan har Rt Hon Tajudeen Abbas (Iyan Zazzau)ya cigaba da jagorancin ta
Agbese Wanda Ya yi wannan bayani jim kadan bayan kammala zaman da majalisar ta yi domin rantsar da sabbin mahukunta a majalisa ta goma da aka kafa