Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i ta ƙasa ASUU, ya ce ba su samu wata sanarwa daga gwamnatin tarayya ba kan zama da Ministan Kwadago, da nufin kawo karshen yajin aikin da suke yi.
Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana hakan a wata hira da yayi da BBC.
Farfesan ya kara da cewa Ministan Kwadago, Chirs Ngige, ne ma ya yi watsi da tattaunawar, ya kuma dakatar musu da albashi da tunanin cewa hakan zai sa su sauya matsayarsu.
A jiya Laraba ne Mistan Kwadago Chris Ngige ya shaida wa manema labarai cewa za su yi wani zama da wakilan ASUU yau Alhamis da nufin kawo karshen tirka-tirkar da ke tsakaninsu, don ganin cewa dalibai sun koma azuzuwansu.
Yanxu haka dai daliban jsmi’o’in Najeriya sun shafe watanni zaune a gida, bayan gaza cimma matsaya tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya.
Comments 1