Ban sayi gidaje ba ko na saci kudin gwamnati na kaisu Dubai – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya dage cewa bai saci kudin jihar zuwa Dubai ba.
El-Rufai ya kuma kalubalanci magabatansa a Jihar da su fito su rantse cewa ba su taba satar dukiyar jihar ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-Yanzu: CBN Ya Amince Bankuna Su Ci Gaba Da Karɓar Tsofaffin Kudi
Tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a cikin harshen Hausa a gidan talabijin da gidan rediyon kasar.
Ya ce, “Na yi farin ciki da mun gina hanyoyi masu inganci da za su dau shekaru. Ba irin wadannan hanyoyi da suka yi a baya ba, wanda bayan shekaru biyu, bayan damina biyu, hanyoyin za su lalace.
“Har yanzu muna da aikin yi. Shirinmu shi ne, muna son a yi kwalta a duk hanyoyin Kaduna. Duk wanda ya zo Kaduna ba zai ga hanyar ƙasa ba.”
Ya kara da cewa, “Mutane na iya ganin cewa mun aiwatar da wadannan ayyuka da rancen da muka yi. Ba mu saci kudin muka kaisu Dubai muka sayi gidaje ko mu je Jabi Road muka gina katafaren gida ba.
“Ba mu zama kamar irin waɗannan mutane ba. Na zama Gwamnan Jihar Kaduna da gida daya a titin Danja a Unguwan Sarki Kaduna. Na gama wa’adina, Alhamdulillah…wato gidana daya tilo. Ba ni da wani gida. Ban gina babban gida ba. Ba ni ma bukata.”
A wani labarin kuma:Kotu Ta Daure Wani Uba Bayan Ya Haikewa Ɗiyarsa Mai Shekaru 18
Wata Kotun Majistare da ke Ikeja a Ogba din Jihar Legas, ta tasa keyar wani mutum mai shekaru 36, Roland Okajere, zuwa gidan yari na Kirikiri.
Ana zargin mutumin ne da yi wa ‘yarsa ‘yar shekara 18 fyade a cikin shagonsa da ke yankin Ikotun a jihar.