Ban Taɓa Sukar Naɗin El-Rufa’i A Matsayin Minista Ba – Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya musanta cewa ya ki amincewa da wanda ya gabace shi, Nasir El-rufai a matsayin minista.
DAILY POST ta tuna cewa an soke zaɓen El-Rufai ne a yayin tantancewar sakamakon rashin kammala binciken tsaro.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yan sandan Jihar Ogun sun cafke wani matashi bisa ɓatan kaji 1, 300
Bayan ‘yan kwanaki El-Rufai ya ki amincewa amma ya zabi wanda zai maye gurbinsa.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya fitar ta bayyana cewa rahotannin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne cewa na soki nadin El-Rufa’i, sai dai an yi haka ne da nufin haifar da rashin jituwa tsakanin Uba Sani da El-Rufai.
Gwamnan ya jaddada cewa sahihin abin da ke cikin labarin shi ne ganawar da ya yi da shugaban kasar, inda ya kara da cewa ko kadan a lokacin taron ba a taho da batun wanda zai maye gurbinsa ba.
Don haka ya yi kira ga kafafen yada labarai da masu amfani da shafukan sada zumunta da shafukan yanar gizo da su guji yada bayanan da ba a tantance ba da kuma na karya wadanda za su iya yaudarar masu karatu da kuma haddasa rikicin siyasa a kasar.
Ya kuma bukaci manema labarai da su gane rawar da suke takawa a matsayin sune matakai na huɗu da kuma kiyaye mutunci ta hanyar yada ingantattun labarai da madaidaitan labarai wadanda ke taimakawa wajen ci gaban kasa.
A wani labarin kuma:Taɓa Ganduje Da Ka Yi Shiyasa Ka Rasa Kujerar Minista – Jigon APC Ga Kwankwaso
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta bayyana cewa caccakar da ake ci gaba da kaiwa ga kyawawan ayyukan shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Abdullahi Ganduje a jihar Kano, suna iya zama silar rasa kujerar minista ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigerian People’s Party, Sanata Rabi’u Kwankwaso a majalisar ministocin shugaban kasa. Bola Tinubu.
Kafin kaddamar da wadanda Tinubu ya nada a matsayin ministoci, akwai shawarwarin cewa Kwankwaso zai iya samun mukami a gwamnatin Tinubu, ganin irin ‘yan uwantaka da ke tsakanin ‘yan biyu bayan zaben shugaban kasa.