Bankuna, otal -otal har ma da gine -ginen jama’a sun cire tutar Nigeria daga cikin gine -ginensu, saboda bin umurnin kungiyar Masu fafatukar kafa kasar Biyafara wato IPOB.
Kungiyar, wacce ke addabar jihohin Kudu maso Gabas, ta sake ayyana dokar zaman a gida a ranar 1 ga Oktoba shekarar 2021, kuma ta ba da umarnin cire tutocin Nigeria a dukkan gine-gine masu zaman kansu da na gwamnati a yankin.
Wani babban jami’in daga kungiyar IPOB Chika Edoziem, a ranar Juma’a ya ce, zai kulle dukkan yankin Kudu maso Gabas a ranar 1 ga Oktoba shekarar nan.
“Ranar 1 ga watan Oktoba, mun ayyana rufe baki dayan a kasar Biafra. Babu wani motsi a kasar Biafra a ranar 1 ga watan Oktoba ranar samun ‘yancin kan Nigeria. Har ila yau daga daren yau, duk tutocin Nigeria, da aka dora a ko ina a cikin kasar Biafra, dole ne a sauke su,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Mutum 3 da jikkata wasu a Filato
“Bangaren Shugabancin IPOB zai yi magana da bankunan kai tsaye, kuma za ta ba su dalilin da ya sa dole su sauke tutar cikin lumana. In ba haka ba, mu da kan mu, mu cire ”a cewar shi.
Idan za’a iya tunawa cewa, Hukumar tsaro ta Farin kaya DSS ta tsare shugaban kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, bayan kama shi a kasar Kenya.