Gwamnan jihar Benue, Rabaran Fr. Hyacinth Alia ta yi Allah-wadai da hare-haren ‘yan fashi da makami a wasu bankunan kasuwanci a garin Otukpo.
DAILY POST ta rawaito cewa ‘yan bindigar masu dauke da manyan manyan makamai sun kai farmaki akalla bankuna hudu a garin inda suka yi awon gaba da wani adadi na kudade da ba a tantance adadinsu ba.
‘Yan fashin dai a yayin samamen da aka dauki tsawon sa’o’i ana yi, sun yi awon gaba da kwastomomi akalla shida da ‘yan sanda hudu.
Karanta nanGwamnan Zamfara Ya Nada Kantomomin Riko Na Kananan Hukumomin Jahar 14
Da yake mayar da martani gwamna Alia a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Sir Tersoo Kula ya fitar a ranar Asabar ya bayyana lamarin fashin a matsayin cin mutuncin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa an kai hare-haren ne a daidai lokacin da taron kwamitin tsaro ke gudana a gidan gwamnati dake Makurdi babban birnin jahar.
Alia ya jajanta wa iyalan wadanda barayin suka yi wa kisan gilla a lokacin fashin inda ya basu tabbacin rashin sake faruwar hakan.
Ya ce abin takaici ne yadda ’yan fashin marasa hankali suka bindige mutanen da suke bakin aiki, musamman jami’an ‘yan sanda, har lahira.
Amma ba za su iya tserewa da wannan ba domin nasan tuni dai hukumomin tsaro na kan hanyarsu don haka dole ne a kama su a gurfanar da su a gaban kotu.
A wani labarin kumaDiyar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Borno,Ana Zargin Mijinta-Yan Sanda
Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar da su kasance masu lura kuma a kodayaushe su himmatu wajen ba da rahoton duk wani motsi da suka ji kusa dasu da basu yarda dashi ba.
Ku tabbatar kun kai rahoton duk wani abu da baku amince dashi ba a gaban hukumomin tsaro domin daukar mataki inji gwamnan.