Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar Labour ta ce Gwamna Nyesom Wike wanda yake barazanar rufe otal-otal da wuraren shakatawa ya biyo bayan fargabar rasa madafun iko a jihar.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa na shiyyar Kudu-maso-Kudu, Felix Reuben ne ya yi wannan ikirarin yayin da yake zantawa da manema labarai a Fatakwal a ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Sheikh Goni Aisani, Ya Bukaci A Hukunta Jami’an Sojin
Yayin da yake yin Allah-wadai da barazanar da gwamnan ya yi, shugaban jam’iyyar ya ce Wike zai wuce karfinsa ta hanyar lalata harkokin kasuwanci.
A cewarsa, “Abin da yake yi shi ne ya tsorata masu otal da kuma jam’iyyun siyasa daga gudanar da taro. Duk abin da gwamna ke yi, yana yi ne saboda tsoro kuma ina ganin ya fi karfin ikonsa.”
“Mutanen Jihar Ribas na bukatar su kira shi su ba shi umarni domin wata rana zai bar kujerar, kuma idan aka yi masa irin wannan aiki, ba na jin zai yi da kyau.”
“Don haka, duk abin da gwamnati ta ce, ina yin Allah-wadai da shi gaba daya, kuma mun yi imanin abin da yake yi na kishi ne da tsoron rasa ikon jihar Ribas.”
“Muna yin Allah-wadai da duk abin da gwamnati ke cewa game da ruguza otal din mutane.”
“Waɗannan rayuwar mutane ne. Idan wani ya yi taro a cocin mahaifinsa yau, zai je ya rushe cocin?”
A wani labarin kuma Najeriya Tana Fitar Da Kayayyakin Da Ba Na Man Fetur Ba Da Darajarsu Ta Kai Dala Biliyan 2.6 – NEPC
Hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta Najeriya (NEPC), a ranar Talata ta bayyana cewa, Najeriya ta fitar da sama da tan miliyan 4.146 na kayayyakin da ba na mai ba, wanda darajarsu ta kai dala biliyan 2.593 daga watan Janairu zuwa Yunin 2022.
Babban daraktan NEPC, Dr Ezra Yakusak ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da rahoton ci gaban rabin shekarar 2022 ga manema labarai a Abuja.