Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP ya yi watsi da barazanar da magajinsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi na shan alwashin zai iya marinsa idan suka hadu a Aso Rock da ke Abuja.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kwankwaso ya ce Ganduje yana daya daga cikin yaransa a siyasance kuma bai zai iya hada ido da shi fuska da fuska ba.
Rabi’u Kwankwaso da Ganduje sun ziyarci shugaban Kasa Bola Tinubu lokaci daban-daban a ranar Juma’a. Yauin da yake zantawa da manema labarai Ganduje ya ce zai iya zabga wa tsohon maigidansa mari da sun hadu a Villa.
KARANTA WANNAN Idona Idon Kwankwaso A Villa Sai Na Wanke Shi Da Mari — Ganduje
“Na ji shi (Ganduje) ya ce zai mare Ni, amma ina nan. Ya rude ne kawai. Wadannan duk yarana ne a siyasance. Ba ma iya kallona zai yi katsaye ba idan muka hadu” Kwankwaso ya shaida wa BBCHausa.
Ya kuma tabbatar da cewa ya tattauna da shugaban Kasa Bola Tinubu kan yiwuwar shiga cikin gwamnatinsa.
A cewar Kwankwaso, Tinubu ya yi masa tayin nadi amma har yanzu bangarorin biyu ba su kai ga cimma matsaya ba.
“Mun tattauna domin hadin gwaiwa, duk da haka, an yanke shawara mai muhimmanci. Bayan kaddamar da majalisar Kasa, za mu tantance abun da ya dace” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma jaddada cewa matsayin da Tinubu ya ba shi na tuntubar juna ne, kuma hakan ba yana nufin zai fice daga jam’iyyar NNPP ba.
Ya ce nan da makwanni biyu za a bayyana matakin karshe da suka yanke ga al’umma.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Dangane da rusau da ake yi a Kano, Kwankwaso ya bayyana cewa ya yi wa shugaban Kasa bayani kuma an samu fahimtar juna.
Acewarsa, Tinubu ya bayyana gamsuwa da matakin da gwamnatin Kano ta dauka akai.
A Wani Labarin Kuma Sojoji Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda 6, Sun Kwato Makamai – DHQ
Shedikwatar tsaro ta ce dakarun Operation Forest Sanity tare da hadin gwiwar shedkwatar rundunar tsaro ta musamman, sun kashe ‘yan ta’adda shida tare da kwato makamai da alburusai a jihar Kaduna.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manji janaral Musa Danmadami, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.