Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun kaddamar da wani tsari mai ginshikai guda uku da zai shirya, ganowa da kuma magance matsalolin dake bukatar kulawar gaggawa a yayin da aka samu barkewar cututtuka. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Da yake kaddamar da shirin a garin Damaturu na jjihar Yobe, babban mai ba da shawara kan magance cututtukan a ma’aikatar lafiya ta kasa, Dokta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa, taken shirin shi ne ‘Karfafawa da Amfani da Kungiyoyin Ba da Agajin Gaggawa da nufin inganta shiri da hadin kai a duk matakai.
KU KARANTA: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Samu Sabon Shugaba
Jihar Yobe da ke farfadowa daga hare-haren Boko Haram, na fuskantar wasu iftila’i da ke fadawa bil’adama da dabi’a.
A shekarar 2022 kadai, mutane 74 ne suka mutu yayin da hekta 30,000 na gonaki suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifat, yayin da gidaje 35,000 suka rasa nutse a fadin jihar duk da gargadin da hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya NIMET ta yi.
Kwamishinan lafiya na jihar Yobe, Lawan Gana, a nasa jawabin, ya yi maraba da shirin, inda ya bayyana cewa, duk da kokarin da ake yi, jihar na fuskantar karancin kwararrun ma’aikata da karancin kayan aiki.
Shirin wanda aka kaddamar a shiyyoyin kasar nan shida, ana sa ran zai bunkasa fannin kiwon lafiyar jama’a, da kai dauki cikin gaggawa kuma a lokaci da ake bukata ga duk wani lamarin dake bukatar kulawar gaggawa.
A wani labarin kuma, Matatar Man Dangote Za Ta Taimaka Wajan Inganta Wutar Lantarki A Nahiyar Afrika–Shugaban Senegal
Shugabannin kasashen Ghana, Nijar, Senegal, Togo da kuma Chadi sun jinjinawa shugaban rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote kan kafa matatar mai a kasar nan. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Shugabannin da suka gana da takwaransu na Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari, a wajen kaddamar da matatar Mai, mai karfin tace litita 650,000 a yankin Lekki da ke jihar Legas, sun ce matatar mai da ke daya daga cikin mafi girma a duniya za ta kara habaka a nahiyar Afirka.