By Abbas Yakubu Yaura
Alhaji Bashir Tofa, daya daga cikin ’yan takara a zaben shugaban kasa na shekarar 1993, wanda aka ce mafi yanci da adalci a kasar, ya rasu.
Har yanzu babu cikakken bayani game da rasuwarsa amma an ce dattijon ya yi jinya na wani dan lokaci.
Daya daga cikin ‘ya’yan Tofa, wacce ta karyata jita-jitar mutuwarsa a lokacin da aka rika yada jita-jita a shafukan sada zumunta kwanaki uku da suka gabata, ta tabbatar da rasuwarsa a safiyar ranar Litinin.
Har zuwa rasuwarsa, Tofa ya shahara da yin magana ga kasar da kuma ba da shawarwarin da za a iya magance wasu matsalolin da suka shafi Najeriya ta hanyar su.
Tofa, dan takarar jam’iyyar NRC a zaben shekarar 1993, ya fafata da Marigayi MKO Abiola na jam’iyyar (SDP).
Jaridar Aminiya ta fahimci cewa ana shirin binne mamacin, inda wata majiya daga dangi ta ce za a binne shi da misalin karfe tara na safe.
An haife shi a ranar 20 ga watan Yunin shekarar 1947, Tofa ya yi karatun firamare a Shahuci Kano, sannan ya ci gaba da karatu a City Senior Primary School da ke Kano.
A tsakanin shekarar 1962 zuwa 1966 ya halarci kwalejin lardi da ke Kano. Bayan ya kammala karatunsa a makarantar lardi, ya yi aiki da kamfanin inshora na Royal Exchange daga shekarar 1967 zuwa 1968. Sannan kuma Daga shekarar 1970 zuwa 1973, ya halarci Kwalejin City dake birnin London.
Batunsa na siyasa ya faro ne a shekarar 1976 lokacin da aka zabe shi kansila a karamar hukumar Dawakin Tofa. A cikin shekarar 1977, an zabe shi mamba a Majalisar Zartarwa. A lokacin jamhuriya ta biyu ta Najeriya, Tofa a lokuta daban-daban ya kasance sakataren jam’iyyar NPN reshen Kano, daga baya ya zama sakataren kudi na jam’iyyar na kasa kuma ya kasance
mamba na kwamitin koren juyin juya hali na kasa.