Da yake hana wani sauyi a minti na karshe, tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye, zai bayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar sanatan Filato ta tsakiya a jam’iyyar Labour Party (LP).
Dariye; A ranar Litinin ne aka sako tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame, da wasu mutane uku daga gidan yari watanni uku bayan afuwar da majalisar kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi, a ranar 14 ga Afrilu, 2022.
Dariye, wanda ke zaman gidan yari na shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan 1.126, an sake shi bayan kimanin shekaru hudu a gidan yari.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito daga majiya mai tushe cewa Jam’iyar LP reshen jihar Filato ta kammala shirye-shiryen karbar tsohon gwamnan Filato daga Abuja domin karbar fom din takarar sanata na jam’iyyar.
Dariye wanda ya taba zama gwamnan a jam’iyyar PDP ya fice daga jam’iyyar.
Wani jami’in jam’iyyar Labour, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce: “Eh, gaskiya ne shi (Dariye) zai tsaya takarar kujerar Sanata. Muna shirye-shiryen zuwan shi daga Abuja domin yin shelar Sanata”.
Majiyar ta ce Dariye zai ba da mamaki a zaben saboda ana ci gaba da kaunar sa a jihar.
Majiyar ta ce komawar Dariye ya kuma kara wa dan takarar gwamna na jam’iyyar, Patrick Dakum, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour, bayan da ya kasa samun tikitin takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Sai dai fuk kokarin da manema labarai sukayu wajan ji ta ankin Shugaban jam’iyyar Labour Party na jihar Filato, Honarabul Grace Zamfara, abun ya citura.