Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu a karkashin jam’iyyar NNPP, Lawal Yahaya Gumau, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
Gumau wanda tsohon dan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazabar Toro ta tarayya ya tsaya takarar sanata a karkashin jam’iyyar APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci Kan Sauya Fasalin Naira
Sai dai bayan ya kasa samun tikitin tsayawa takarar kujerar Sanata a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023, sai ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP inda ya samu tikitin bayan da sabani ya kaure tsakaninsa da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a yanzu, Yakubu Shehu. .
An ce shugabannin jam’iyyar NNPP na kasa da kuma dan takararta na shugaban kasa, Rabi’u Kwankwaso sun fifita shi a gaban Shehu.
Amma bayan da ya sha kaye a zaben da ya gabata a majalisar dattawa kuma a fili saboda yadda jam’iyyar NNPP ta gudanar da zabubbukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ta kasa, dan majalisar tare da ko-odinetocin yakin neman zabensa da magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar suka koma PDP mai mulki a Bauchi.
Ya bayyana sauya shekar sa zuwa jam’iyyar PDP ne a yayin wata tattaunawa da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.
Dan majalisar ya bayyana goyon bayan sa ga takarar Mohammed ta sake tsayawa takara sannan kuma ya umurci magoya bayan sa a fadin yankin sa na majalisar dattawa da su kada kuri’ar zaben gwamna da daukacin ‘yan takarar majalisar tarayya a zaben na ranar 11 ga watan Maris.
Ya ce gwamnan ya yi aiki fiye da yadda ake tsammani, don haka akwai bukatar kowa da kowa ya ba shi goyon baya don samun nasarar sake zabensa na sake gudanar da ayyukan raya kasa don amfanin jihar da al’ummarta.
“Abu mafi mahimmanci ba batun jam’iyya ba ne, halayya ce ta jawo mu cikin jam’iyyar. Na koma PDP ne saboda Kauran Bauchi wanda shi ne shugabana kuma jagorana kuma mutum ne wanda a kullum nake bi don in samu nasara a siyasa.
“Na koma bangaren gwamna ne a yanzu saboda ina son jama’ata su ji tasirin dimokuradiyya, kuma bayan na yi bincike na gano cewa Kauran Bauchi ne ya fi kowa, kuma ayyukansa ne ya sa muka zo wurinsa.
“Magoya bayana su gode wa Allah da ya ba mu amintaccen shugaba wanda za mu iya dogara da shi. Gwamna Bala Mohammed wani irin shugaba ne wanda ko ba tare da ya tambaye shi ba zai tuna cewa yana da hakki a kansa.
“Ba lallai ba ne ya yi aiki a kan abin da mutane suka roke shi ya yi, yana yin abin da ya ga yana da kyau ga jama’arsa don haka dole ne mu zabi Gwamnan Bala domin ba shi damar ci gaba da gudanar da ayyukansa na alheri ga jiharmu ta Bauchi,” inji shi.
Gwamna Bala Mohammed, a martanin da ya mayar ya tarbi Gumau da daukacin magoya bayansa da masu gudanar da yakin neman zabensa zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar, ya kuma yi alkawarin samar musu da filin wasa domin bayar da gudumawa mai kyau wajen samun nasarar dukkanin ‘yan takarar sabuwar jam’iyyarsa a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha masu zuwa a jihar.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Atiku da Obi Sun Kai Kara Kotu, Sun Bukaci A Duba Kayan Zabe
‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da na Labour Party, Atiku Abubakar da Peter Obi sun garzaya kotun saurarar karar zaben shugaban kasa domin neman izinin duba kayan zaben da aka yi amfani da su a zaben na ranar Asabar da ta gabata.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Atiku da Obi sun ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, inda suka sha alwashin garzayawa kotu.