Manyan ‘yan kasuwa masu zaman kansu na PMS wanda aka fi sani da man fetur sun kara farashin famfo a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Punch ta rahoto.
Wasu gidajen mai da wakilinmu ya ziyarta a ranar Talata ya bayyana cewa suna sayar da man kan kowace lita a tsakanin N545 zuwa N700.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Farashin Man Fetur Ya Koma N617 Kan Kowacce Lita
Wasu gidajen mai da aka ziyarta sun hada da NIPCO wanda yake sayar da lita daya kan Naira 545; ya yinda gidan mai na Shafa Energy yake cefanarwa akan N595.
Sannan gidan man Rainoil kuwa yana sayarwa akan N568, ina da gidan man Emmanuel ke sayarwa kan N560 shi kuwa Neeman yana sayarwa akan N700.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Tinubu Zaiyi Nazari Kan Bada Tallafin Kudi Naira 8,000
Shugaba Bola Tinubu, a ranar Talata, ya ce gwamnatinsa za ta sake duba shirinta na farko na raba tallafin kudi na Naira 8,000 duk wata ga gidaje miliyan 12 na tsawon watanni shida a wani bangare na kokarin rage wahalhalun da tallafin man fetur ya haifar.
Wannan ya biyo bayan sukar da jama’a da dama suka yi wa manufar tare da kungiyoyin kwadago da ke cewa ta yi nisa da matakin shiga tsakani da ake bukata don ragewa ‘yan Najeriya masu rauni radadi .
“Shugaban kasa ya ba da umarnin cewa… kudi naira 8,000 da aka tsara don bada tallafi ga mafi yawan matsugunan gidaje za a sake duba su nan take,” a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman, Dele Alake, ya sanyawa hannu a ranar Talata.
Alake ya ce sabon umarnin “biyyana ne ga ra’ayoyin da ‘yan Najeriya suka bayyana a kansa.”
Tinubu ya ba da umarnin cewa a bayyana wa ‘yan Najeriya baki daya tsarin tafiyar da gwamnati.