An saki tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Abdurasheed Bawa daga inda yake a tsare.
Idan zaku tuna cewa Hukumar DSS ta kama Bawa ne a ranar 14 ga watan Yuni, 2023, sa’o’i bayan dakatar da shi daga mukaminsa na Shugaban Hukumar EFCC da Shugaba Bola Tinubu ya yi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.
An sako Bawa ne a daren Laraba daga hedikwatar ‘yan sandan sirri ta kasa da ke Abuja.
Karanta nan‘Yan Bindiga Sun Sako Malamar Jam’iar Nasarawa Da Suka Sace
Rundunar ‘yan sandan sirri ba ta fito fili ta shigar da kara a gabanta ba ko kuma bayyana irin laifin da ya aikata tun bayan kama shi da tsare shi.
Ba a iya samun mai magana da yawun hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, da na EFCC Dele Oyewale domin jin ta bakin Bawa a lokacin da aka mika wannan rahoton.
Kafin kama shi, wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Willie Bassey, ta ce dakatarwar da aka yiwa Bawa ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafin ofishinsa da aka yi masa.
Bassey ya bayyana cewa, an umurci Bawa da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Daraktan ayyuka a hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin shugaban hukumar, har sai an kammala bincike.
A wani labarin kumaAn Shiga Fargaba Yayin Da Fursunoni Suka Tsere Daga Kurkuku A Katsina
Sanarwar ta ci gaba da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da dakatar da Mista AbdulRasheed Bawa, CON daga ofishin Mista AbdulRasheed Bawa, a matsayin shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) don ba da damar gudanar da bincike mai kyau kan yadda ya aikata yayin da yake kan mulki.
Wannan ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da aka yi masa a lokacin da yake jan ragamar hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.