- Majalisar dokokin Ondo, ta tabbatar da samun takardar komawa bakin aiki daga gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu
- Matakin na gwamnan ya yi dai dai da sashe na 190(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya
- Tuni daukacin al’ummar jihar suka nuna jin dadin dawowar sa kan karagar mulki
Majalisar dokokin jihar Ondo, a ranar Juma’a ta tabbatar da samun takardar komawa bakin aiki daga gwamnan jihar, Mista Rotimi Akeredolu, wanda ya dawo daga hutun jinya a kasar Jamus.
Kakakin majalisar dokokin jihar Rt.Hon.Olamide Oladiji,shi ne wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, Tribune Online ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Gwamnati Ta Dawo da Basaraken Gargajiya, Ta Bukaci Fusatattun Sarakuna Su Kwantar da Hankula
Kakakin majalisar ya ce matakin na gwamna Akeredolu ya yi daidai da sashe na 190(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (kamar yadda aka gyara).
Shugaban majalisar ya bayyana cewa gwamnan ya koma bakin aiki ne a ranar Juma’a 8 ga watan Satumba, 2023, inda ya ce an samu wasikar ne yayin zaman majalisar na jiya.
A cewar shugaban majalisar, “Gwamnan a cikin wasikar ya bayyana godiya ga ‘yan majalisar bisa fatan alherin da suka yi.”
Oladiji ya ce “Aikin Gwamnan ya yi daidai da sashe na 190 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya (kamar yadda aka gyara).
“An samu wasikar ne a yau yayin zaman majalisar, gwamnan ya koma bakin aiki yau Juma’a, 8 ga Satumba, 2023.”
Oladiji, wanda ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya dawo da gwamnan gida lafiya, ya ce daukacin al’ummar jihar Ondo na jin dadin dawowar sa kan karagar mulki.
A halin da ake ciki, babban sakataren yada labarai na gwamna Akeredolu, Mista Richard Olatunde, a ranar Juma’a, ya tabbatar da dawowar gwamnan kasar daga hutun jinyar da ya yi.
A wani labarin kuma, Tsaro: Sarkin Birnin Gwari Ya Sauya wa Wasu Hakimai Fada
Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Jibril, Maigwari Il, ya amince da sauya wasu Hakimai biyu a masarautarsa
Zamu goyi bayan duk wani mataki da mai martaba sarkin ya dauka na kawo karshen kalubalen tsaro
Tuni hakiman suka fara aiki cikin gaggawa
A ci gaba da kokarin inganta harkar tsaro a Masarautarsa, Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Jibril, Maigwari Il, ya amince da sauya wasu Hakimai biyu a masarautarsa.
Wata sanarwa da sakataren masarautar Mukhtar Salisu Muhammad ya fitar kuma aka aikawa Tribune Online ta bayyana cewa hakimai biyu za su yi musanyar mukaman.