Shugaban Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere, Pa Ayo Adebanjo, yace bazai taɓa yin imani da Babban zabe mai zuwa na shekarar 2023, a dalilin taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.
Ya bayyana haka a ranar Juma’a a lokacin da yake tattaunawa da majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya, akan bikin murnar cikar Najeriya shekaru 61.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum ɗaya ya mutu, mutane biyar sun jikkata, a yayinda motoci takwas suka ƙone a wani hatsari a Abuja
A lokacin da aka tambaye shi akan shugaban ƙasar da Nigeria ta kamata ta samu, Adebanjo yace, “baiyi imani da Babban zabe na shekarar 2023, don haka bazan taɓa amincewa da yadda ake fama da matsalar tsaro a ƙasar, daya haɗa da kashe-kashe, da garkuwa da mutane, da fyaɗe, kuma ayi zaɓe.”
An ƙone da yawan ofisoshin ƴan sanda, dana Hukumar zaɓe mai zaman kanta a watanni da suka gabata, wanda suka kai hari a gine-ginen gwamnati, musamman a kudancin Nigeria, inda ake cigaba da yin gwagwarmayar raba ƙasa.