By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta bayyana cewa ta tura jimillar jami’ai dubu daya da dari uku da talatin da shida a wuraren da jama’a ke taruwa domin tabbatar da gudanar da bukukuwan ba tare da cikas ba a duk lokacin bukukuwan Ista.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Mista Odiko MacDon ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Juma’a a Uyo, babban birnin jihar.
DUBA WANNAN LABARIN: Shehu Sani Ya Aika Sako Ga Okocha, Kanu, Da Sauransu Kan Kauracewa Harkokin Wasanni A Najeriya
MacDon ya tabbatar wa mazauna yankin da kuma masu ziyara cewa rundunar za ta ci gaba da samar da dabarun tsaro na zamani don inganta tsaron jihar.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da zama masu bin doka da oda, inda ya kara da cewa umurnin zai hada kai da Kiristocin jihar domin gudanar da bukukuwan Easter lafiya.
Kazalika Ya ci gaba da cewa: “Don samar da yanayin gudanar da bukukuwan Ista, kwamishinan ‘yan sanda, Mista Andrew Amiengheme ya tura jami’ai dubu daya da dari uku da talatin da shida (1,336) domin karfafa tsaro a fadin jihar.
musamman a Coci-coci, Cibiyoyin Nishaɗi, Wuraren Motoci da kuma kula da zirga-zirga.
“Rundunar ta CP tana taya gwamnati da daukacin ’yan jihar Akwa Ibom, musamman al’ummar Kirista murnar bikin Easter, tare da yin kira ga mutanen jihar da su ci gaba da bin doka da oda tare da kai rahoton masu aikata laifuka da ke da niyyar dakile zaman lafiya da ake samu a Jihar.
“Rundunar tana so ta tabbatar wa mazauna yankin da masu ziyara cewa za ta ci gaba da samar da dabarun tsaro na zamani don inganta tsaron jihar.
“Lokacin da ake cikin damuwa ko don dalilai na bayanai, ana shawartar jama’a da su yi amfani da lambobin gaggawa wajen kiran jami’an Rundunar; 080-392-13071 da 080-813-88797”
Comments 1