Gwamann Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi afuwa ga fursunoni 100 a ci gaba da bukukuwan Karamar Sallah a jihar.
Ganduje ya yi musu afuwa ne a yayin ziyarar Sallah da ya jagoranci ’yan Majalisar Zartarwar Jihar Kano tare da shugabannin siyasa da wasu manyan mutane zuwa Gidan Yarin Goron Dutse a ranar Litinin.
Gwamnan ya yi alkawarin “Sakin karin fursunonin nan da kwanan 70, wato lokacin Babbar Sallah,” yana mai umartar wadanda aka sallama da su je gwamnati ta yi musu rajista domin koyon sana’o’in dogaro da kansu.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Abba Anwar, ya firtar ta bayyana cewa dalilan yi wa fursunonin afuwa sun hada da: “Rashin lafiya da tsufa da kuma rashin iya biyan tarar da kotu ta yi musu; Sai dai rahotanni sun nuna cewa, a cikin akwai wadanda aka yanke wa hukuncin kisa.
Gwamnan ya bayyana cewa an yi musu afuwa ne domin ba su dama su gyara halayyarsu su zama mutane nagari, gami da rage cunkoso a gidajen yarin dake jihar ta Kano.
A wani labarin Kuma na daban
Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne an banka musu wuta inda suka kone kurmus a garin Kanshio da ke wajen garin Makurdi a jihar Benue.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, an bi su ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda aka kama su daura da makarantar Divine Mercy Minor Seminary da ke Kanshio inda a karshe aka kona su.
An tattaro cewa wadanda ake zargin wadanda tun farko su uku ne amma daya daga cikinsu ya tsere a lokacin da ake binsa, sun samu shiga wani gida da karfi da yaji a garin Kanshio a kokarinsu na yi wa dangi fashi bayan sun yi harbin gaggawa don kaucewa shiga tsakani.
Sai dai kuma sa’a ya ci karo da su, inda aka ce shugaban gidan ya yi ta maza inda ya kama daya daga cikinsu, lamarin da ya sa sauran mutanen biyu suka shiga tsakani da wannan jarumin har suka kubutar da abokin aikin nasu.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wadanda ake zargin bayan ceto dan kungiyar nasu ne suka gudu ta hanyar tsallaka katanga inda suka hau kan babur da ke jiran su a bakin titi amma wadanda abin ya shafa suka nemin taimakon mazauna yankin lamarin da ya jawo hankalin wasu matasa da ke yankin.
Matasan dai kamar yadda aka samu sun fatattaki wadanda ake zargin har ta kai da biyu daga cikinsu suka makale a kusa da makarantar Seminary inda nan take suka banka musu wuta yayin da sauran suka tsallake rijiya da baya ta katangar makarantar suka tsere.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Benue PPRO, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.
“An tabbatar da al’amura. Ana ci gaba da bincike, don Allah, ”in ji Anene a cikin wani sakon rubutu.