Gwamnan Borno Babagana Zulum ya umurci jami’an tsaro da su murkushe ’yan kungiyar Marlian da ake kyautata zaton suna addabar jama’a a wasu sassan Maiduguri da Jere da ke cikin birnin jhar, Daily Post ta rawaito.
Kungiyar ta Marlian wadda wasu matasa ke da alaka da shaye-shayen miyagun kwayoyi, ta yi kaurin suna wajen aikata laifuka da dama da suka hada da karbar kudi, fashi da makami, da safarar miyagun kwayoyi, da ayyukan ta’addanci da suka hada da kashe jami’an tsaro.
KARANTA WANNAN: Shugabannin APC Zasu Gana Kan Muhimmin Batun da Ya Taso
Gwamna Zulum, a ranar Laraba a Maiduguri, ya gudanar da wani taron tsaro na gaggawa a gidan gwamnati, daga bisani kuma ya yi wa manema labarai karin haske.
“Na kira wannan taron majalisar tsaro na gaggawa ne domin magance matsalar tsaro da ta kunno kai a cikin birnin Maiduguri da wasu sassan karamar hukumar Jere, da nufin fito da wasu hanyoyin da za a iya aiwatar da su domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ake bukata.” Inji Zulum.
“Rahotanni na sirri da ke gaban ofishina daga majiyoyi daban-daban sun nuna karuwar ayyukan ’yan daba da matasa ke yi a wasu sassan babban birnin jihar da kuma karamar hukumar Jere.
“Wannan kungiyar ta kware ba wai kawai a sace wayar da rana tsaka ba, fashi da kuma mallakar makamai na cikin gida, amma a yanzu ta kammala karatun ta na kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da jami’an tsaro,” in ji gwamnan.
Zulum, wanda ya damu matuka game da karuwar tashe-tashen hankula, ya bayyana aniyar gwamnati na maido da zaman lafiya tare da tabbatar da tsaron dukkan mazauna yankin.
“Ina so in tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatin jihar Borno a karkashina ba za ta bari irin wannan lamari ya tabarbare ba.
“Na samu tabbacin jami’an tsaro na dagewa wajen dakile irin wadannan munanan ayyuka, kuma gwamnatinmu ta kasance a kullum da himma wajen tunkarar irin wadannan al’amura cikin kankanin lokaci,” in ji Zulum.
A wani labarin kuma, Shugaban Benin Ya Tafi Kasar Nijar Domin Shiga Tsakani – Shugaban ECOWAS
Shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Tinubu ya ce takwaransa na kasar Benin, Patrice Talon zai tafi Jamhuriyar Nijar ne domin shiga tsakani bayan da masu gadin sa suka yi garkuwa da shugaban kasar Mohammed Bazoum.
A baya dai Vanguard ta rawaito cewa, jami’an tsaron fadar shugaban kasar sun tsare Bazoum a fadarsa da ke Yamai, babban birnin kasar, a wani yunkurin juyin mulki da aka yi a ranar Laraba.