- Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya sha alwashin cewa a mako mai zuwa zai rattaba hannu kan dokar yaki da ‘yan daba
- Matakin ya biyo bayan zartar da kudirin da majalisar dokokin jihar ta yi inda take jiran amincewar Gwamnan
- A karkashin sabuwar dokar, duk mutumin da aka samu da laifin dabar siyasa zai fuskanci dauri na wasu tarin shekaru a gidan yari
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa a mako mai zuwa zai rattaba hannu kan dokar yaki da ‘yan daba domin magance ayyukan da suka shafi ‘yan dabar siyasa a jihar, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da yake kaddamar da cibiyar koyar da sana’o’in hannu ta Biu dake karamar hukumar Biu, inda ya ce majalisar dokokin jihar Borno ta riga ta zartar da kudirin, tana jiran amincewar Gwamnan.
KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan Pa Akinkumi,Wanda Ya Zana Tutar Najeriya
Ya kara da cewa, a karkashin sabuwar dokar, duk mutumin da aka samu da laifin dabar siyasa, za a yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai (7) a gidan yari.
A cewarsa, gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa don magance matsalar tashe-tashen hankulan da matasa ke fama da su domin kaucewa fadawa wani rikici a jihar.
“Gwamnati ta himmatu wajen kawo karshen tashe-tashen hankulan matasa a jihar. Majalisar dokokin jihar Borno ta sake duba dokokin kwamitin da aka yi nazari a kansu na kudin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1994.
“Nan ba da jimawa ba, shugabannin hukumomin tsaro a jihar za su fara ziyarar sanin makamar aiki a dukkanin kananan hukumomin jihar”.
“Da nufin ganawa da iyayen sarakuna da ‘yan uwa kan sabbin dokokin da gwamnatin jihar ta fitar tare da majalisar dokoki,”
Ya bayyana cewa gwamnati ta yanke shawarar gina cibiyoyin koyon sana’o’i a sassa daban-daban na jihar domin samar da ayyukan yi ga kungiyar matasan da ba su da aikin yi domin gujewa ayyukan ‘yan daba.
Ya kara da cewa cibiyar koyar da sana’o’i da ke Biu ta kunshi wuraren bita guda goma sha biyar (15) da aka tanadar da kayayyakin koyon sana’o’i na zamani da suka hada da dinki da zane, gyaran gashi da gyaran fuska, walda, aikin gyaran famfo da gyaran bututu, kafinta, fasahar gini, ayyukan hada lantarki, saka na’ura mai amfani da hasken rana,gyaran motoci da aikin injiniyoyi, fasahar noma, da wuraren horar da ICT da sauransu.
Shima da yake jawabi, kwamishinan ilimi, kimiya, fasaha, da kirkire-kirkire, Injiniya Lawal Wakilbe ya ce gwamnatin jihar ta gina tare da samar da cibiyoyin sana’o’in hannu guda biyar na zamani.
“An biya Naira N4,026,556,644 a matsayin tallafin karatu na kasashen waje da na cikin gida, ya kuma biya Naira N2,485,829,300 a matsayin kudin WAEC da NECO ga daliban da ke makarantun sakandaren gwamnati”.
Gwamnatin jihar Borno ta raba kayan makaranta guda 200,000, da kayan aikin dakunan gwaje-gwaje a makarantu 22, an raba litattafai guda 321,000, kayan makaranta guda 200,000, da kekuna sama da 10,000, a cikin dan kankanin lokaci”.
A wani labarin kuma, EFCC ta Damke Mutane 17 da Ake Zargin Sun Kware Wajen Yin Damfara Ta Intanet
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki zagon kasa EFCC, sun cafke wasu mutane 17 da ake zargi da damfara ta yanar gizo
An dakume wadanda ake zargin ne a yayin wani samame da aka kai bayan samun wasu rahotannin sirri kan masu laifin
Wadanda ake zargin sunyi matukar kwarewa wajen aikata laifuka iri-iri ta yanar gizo
Jami’an rundunar shiyyar Uyo na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki zagon kasa EFCC, sun cafke wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wurare daban-daban a Uyo dake Jihar Akwa Ibom.