Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige murnar cika shekaru 70 da haihuwa a duniya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa, shugaba Buhari ya kuma taya shi murna kasancewarsa jagoran siyasa bisa nasarori da dama da aka samu tare da shi a gwamnatance.
Shugaban, a cikin sakon taya murna ta bakin mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina, a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewa nasarorin da Ngige ya samu sun hada da tasiri a harkokin mulki a matakin jihohi da kasa baki daya.
A cewar shugaban, Ngige ya fara aiki ne a matsayin ma’aikacin gwamnati, inda ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa a majalissar dokoki ta kasa da kuma asibitocin gwamnati, kafin ya shiga harkokin siyasa a shekarar 1999, kuma ya rike mukamin shugaban jam’iyyar, gwamna da kuma Sanata.
Shugaban ya tabbatar da cewa Ngige yana da kwazon da ya sanya yake sha’awar salon mulkinsa, wanda hakan kuma shine silar zaburar da shugabanni.
Buhari ya kuma amince da hangen nesa, sadaukarwa da fahimtar Ngige a kan dokokin kwadago, samar da ayyukan yi, da inganta kyakkyawar alakar aiki tsakanin masu daukar ma’aikata da ma’aikata. Ya ce wadannan kyawawan dabi’u sun haifar da tattaunawa iri-iri tsakanin kungiyoyi da gwamnati, tare da sanya sha’awar ma’aikata a gaba, musamman kan albashi, albashi da alawus-alawus.
To sai dai shugaba Buhari na yabon ministan ne a daidai lokacin da kuma a gefe guda Kungiyar malaman jami’o’i ASUU, ke zargin ministan da hannuna dadewar da suka yi suna yajin aiki.