Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri, Babban Birnin Jahar, domin gudanar da ziyarar kwana ɗaya.
Buhari wanda jirgin sa ya sauka a filin jirgin sama na Rundunar sojin sama, tare da wasu manyan jiga-jigan Gwamnatin sa.
Gwamnan Jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum yana a filin jirgin domin tarbar sa, tare da wasu manyan Hafsoshin Tsaro, wanda tuni suka isa a cikin birnin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Ƴan Sanda Ta Kubutar Da Wani Jariri Dan Wata Uku Da Haihuwa
Shugaban Kasar a karo na biyu a cikin watanni 6 tun ranar 21 ga watan yuni na shekarar 2021, inda ya ƙaddamar da wasu manyan ayyuka da Jahar Borno da Hukumar Cigaban Hukumar Yankin Arewa Maso Gabas.
Shugaban Kasar yana sauka ya isa zuwa Makarantar Shiekh Tijjani Bolori.
Zulum yayi kira ga Al’ummar Jahar dasu fito ƙwansu da kwarkwata domin nuna jindaɗi ga irin ɗumbin ayyukan da Shugaban yayi wa jahar na tsawon shekaru 6.
An kuma lura dacewa dukkanin kasuwanni an umarce su dasu kulle su da hanyoyi, har sai zuwa lokacin da Shugaban Ƙasar ya bar Jahar zuwa ƙarfe 2