A yau Lahadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saurarin cikakken ba’asi kan yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Umaru Sissoco Embalo na kasar Guinea Bissau, Wanda Jami’an soji masu biyayya gareshi suka dakileyunkurin.
Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da a ke ci gaba da taron Shuwagabannin Kasashen kungiyar tarayyar Afrika, dake Gudana a Addis Ababa Babbar birnin Habasha
Babban hadimin Shugaban kasa kan Kafafen yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.
Acewar Adesina, Buhari ya Gana da Babban Ministan kula da harkokin kasashen waje na Kasar Guinea Bissau Suzi Barbosa Wanda ya bajewa Shugaban yadda akayi yunkurin sabawa dokar kasar.
“Sun yi Yunkurin kashe Shugaba Embalo, sun lalata fadar Shugaban Kasar da Harsasai, inda suka kashe mutane akalla 11, sai da aka kwashe kusan awa biyar a na batankashi kafin, a shawo kan mummunan lamari.”
Adesina ya ce Buhari ya yi alkawarin tuntubar sauran shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS, kan yadda za a dawo da zaman lafiya a kasar da ke fama da rikici, cikin kankanin lokaci.