Sanata Shehu Sani ya caccaki gwamnati mai ci da kasa fitar da ‘yan Najeriya miliyan daya daga kangin talauci a maimakon haka ta jefa miliyan 133 cikin matsanancin talauci.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin gwamnati na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.
Babbar Sakatariyar ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Misis Kachollum Daju, ta shaida wa manema labarai a watan Satumba cewa Gwamnatin Tarayya ta yi shirin daukar matakin, idan masu ruwa da tsaki suka taka rawar da ta kamata.
KU KARANTA KUMA Gwamnatin Ta Tace Buhari Ya Tsamo Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Talauci
Amma Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar a ranar Alhamis cewa adadin ‘yan Najeriya da ke fama da talauci ya haura sama da miliyan 133, wanda ke wakiltar kashi 63 cikin 100 na al’ummar kasar.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Sani ta shafinsa na Twitter ya ce gwamnati ta jefa ‘yan Najeriya miliyan 133 cikin talauci a bisa rahotan hukuma.
Ya ce “Sun yi alkawarin fitar da mutane miliyan dari daga kangin talauci; yanzu a hukumance sun jefa mutane miliyan dari da talatin da uku cikin matsanancin talauci.”
A Wani Labarin Kuma An Zargi Shugabannin Tarayya Da Jihohi Kan Talaucin Yan Najeriya – Kwararre
Masana tattalin arziki sun zargi shugabannin gwamnatocin tarayya da na jihohi kan ‘yan Najeriya miliyan 133 da ke fama da talauci.
Wani kwararre kan harkokin tattalin arziki, Mista Idakolo Gbolade kuma Farfesa a fannin tsimi da tanadi a Jami’ar Lead City, Ibadan, Godwin Oyedokun, ne ya bayyana hakan ga DAILY POST yayin da yake mayar da martani ga rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS Multidimensional Poverty.