Buhari Ya Yi Wani Tsokaci Kan Nasarar Da Tinubu Ya Samu A Kotu
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT), wanda ya tabbatar da nasarar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu da ya samu a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwamitin mutum biyar a hukuncin da suka yanke, ya yi watsi da koken ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku da na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Matakin Da Kotun Zabe Ta Yanke Babbar Nasara Ce Ga Jam’iyar Mu-Buhari
Buhari, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, a ranar Laraba, Buhari ya ce kotun ta tabbatar da daɗaɗɗen tarihi.
Ya yi ikirarin cewa hukuncin nasara ce ga jama’a da kuma dimokuradiyya.
A cewar Buhari, alkalan kotun sun yi tsayin daka don tabbatar da adalci kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar ta kara da cewa, “Idan wani ya yi nasara a yau, dimokuradiyya ne da kuma jama’a,” in ji sanarwar, ta kara da cewa “tare da hukuncin Kotun Koli, lokacin zabe ya kare kuma lokaci ya yi da za a mance komai a tunkari gwamnati.
“Daga nan ya kamata sabuwar gwamnatin APC karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta samu goyon bayan kowa domin ganin ta cika alkawuran da ta dauka wa jama’a.
A wani labarin kuma:Abin kunya ne ga Peter Obi, bamu ba – Inji LP kan hukuncin kotu
Wani bangare na jam’iyyar Labour a karkashin Lamidi Apapa ya amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke kan karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peter Obi ya shigar a zaben da ya gabata.
Jaridar DAILY POST ta tuna cewa a ranar Laraba ne kotun ta yanke hukuncin cewa karar da Obi da takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da jam’iyyunsu suka shigar ba su da wata hujja ƙwaƙƙwara kan abinda suke zargi, inda suka amince da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.