Buhari Ya Ziyarci Dahiru Mangal Kan Rasuwar Matarsa
Babban hamshakin dan kasuwa, Alhaji Dahiru Barau Managal, ya ci gaba da karbar muhimman mutane a ziyarar ta’aziyyar rasuwar matarsa.
A ranar Laraba ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bi sahun ‘yan uwa da iyalan marigayiya Hajiya A’isha Dahiru Mangal da ta rasu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Majalisar Dattawa Za Ta Rubutawa Shugaban Kasa Tinubu Wasika Kan Wata Bukata
Ta rasu ne a wani asibiti da ke Abuja a ranar Asabar bayan ta yi fama da rashin lafiya kuma an yi jana’izar ta a Katsina ranar Lahadi.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya raka Buhari gidan Mangal.
Mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa, Tunde Sabiu, na tare da Buhari yayin ziyarar.
Tsohon shugaban kasar ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayiyar ya kuma baiwa iyalan Mangal hakurin jure rashin ta.
Yayin da ya ke Katsina, Buhari, tare da rakiyar gwamna Radda, sun kai ziyarar ban girma da ta’aziyya ga Sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman, a fadarsa.
Haka kuma tsohon shugaban kasan ya halarci taron ci gaban Katsina na shekarar 2023 wanda aka gudanar a gidan gwamnati dake Katsina.
Sauran manyan mutanen da suka je Katsina domin ta’aziyyar sun hada da gwamnonin Kano da Zamfara, Engr Abba Kabir Yusuf Dr Lawal Dauda. Hakan ya kasance baya ga tawagar gwamnonin arewa karkashin jagorancin shugaban su gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe suka ziyarce shi.
Haka kuma a Katsina akwai Jagoran Kwankwasiyya na kasa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi ta’aziyyar.
A wani labarin kuma:Alkalin Alkalai Na Najeriya Ya Sanar Da Abinda Kotun Ke Shirin Yi Wajen Yanke Shari’ar Tinubu, Atiku, Obi
Babban Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Mai shari’a Olukayoode Ariwoola, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ya tattauna ta wayar tarho da Shugaba Bola Tinubu da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, kan karar da ake jira a yanke a kotun sauraren karar zaben shugaban kasa.
Ariwoola ya ce bangaren shari’a ba shi da wani shiri na ganin ya yi wa duk wanda ya shigar da kara rashin adalci ko kuma wadanda ake kara a a goyi bayan su, musamman Tinubu da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP).