Kamfanin Hada Hadar Man Fetur Ta Kasa ta bayyana cewa bukatar shan man fetur da ke akwai tayi matukar raguwa
Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin cire tallafin mai a watan Yuni,jim kadan da karbar mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari
Kafin yanzu gwamnati na kashe Dala biliyan 10 a wajen tallafin mai kafin a cire shi,kudin da yanzu za’ayi amfani dasu wajen yin manyan aiyuka a maimakon kashe su ta hanyar da ba kowane dan Kasa ke amfana ba
Tun bayan cire tallafin mai NNPC ta bayyana cewar bukatar man ya ragu zuwa lita miliyan 48.43 a duk yini ba kamar yada aka saba amfani da lita miliyan 63.21 a watanni biyu da suka gabata ba inji jaridar Leadership News
KARANTA NANMmesoma Ta Bayyana Yadda Ta Samu Maki 362
NNPC ta bayyana cewa hakan baya rasa nasaba da rashin kudi a hannun mutane da kuma kudin da man ya kara da kusan kashi dari
Cire tallafin man da sabuwar gwamnatin Tinubu tayi ya sa farashin litar mai ta tashi da kashi 93℅ a kasuwar bayan fage inda ta tashi da kashi 81℅ a gidajen man Gwamnati
Makwabtan Kasashen kamar Kamaru,Benin da Togo wadanda ke dogaro da man fetur da ake simogala daga Najeriya sun bayyana matukar tsadar da mai yayi sakamakon cire tallafin
A WANI LABARIN KUMA
Student Loan-Kada Kuyi Amfani Da Wannan Damar Ku Kara Kudin Makaranta-Majalisa Ga Jami’oi
Majalisar Wakilan Najeriya sun fadi da babbar murya cewar kar a sake sanadiyar bashin karatu da zaa baiwa dalibai a kara kudin makaranta
Dan Majalisa daga Jahar Benue Teseer Agbu ya bayyana hakan yayin wani zama da majalisar tayi a jiya Alhamis inda ya ce bashin da zaa baiwa dalibai bai zama dalilin da zai sa a kara kudin makaranta a manyan makarantu na Gwamnati dake fadin tarayyar Najeriya ba