Shahararren mawakin Najeriya kuma mai shirya fina-finai, Damini Ebunoluwa Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, ya lashe kyautuka biyu na lambar yabo ta Music Of Black Origin (MOBO) na 2022.
Kyautar nau’ikan biyu sune mafi Best International Act and the Best African Act.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Kori Shugaban Hukumar NIRSAL
An gudanar da bikin karramawar, wanda ya nuna mafi kyawun kade-kaden bakaken fata, an gudanar da shi ne a ranar Laraba a birnin Landan, a filin wasa na Wembley.
An zabi mawakin ne a cikin jerin mawakan kasa-da kasa tare da Chris Brown, Beyonce, Kendrick Lamar, Jack Harlow, Drake, Summer Walker.
Burna kuma ya samu nasarar lashe kyautar ta Afrika ne, inda ya doke Asake, Rema, Fireboy, da Omah Lay.
Wannan ya kawo lambar yabo ta MOBO na mawakin zuwa jimillar guda uku sakamakon nasararsa a 2021.
A wani labari kuma, Ku Dai Na Isgilanci Da Ikon Allah — Keyamo Ya Caccaki Masu Sukar Lafiyar Tinubu
Karamin Ministan Kwadago da samar da Aiki ayyukan yi Festus Keyamo, ya gargadi ‘yan Najeriya kan sukar yanayin lafiyar dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu. Kamar yadda Dialy Post ta ruwaito.
Keyamo ya ce ya kamata masu suka su daina wasa da Allah akan lafiyar Tinubu ko rayuwar sa.
Ya jaddada cewa wadanda ke sukar lafiyar Tinubu ba yi yakin neman zabe na zuwa jiha-jiha da kuma taron wasu manyan taruka ba.
A cikin jerin sakonnin twitter, Keyamo ya wallafa cewa: “Wadanda suke yin kamar su Allah ne kuma suna izgili ne, ta hanyar nuna cewa yana da rauni ba su yi komai ba kamar yadda yaje Jihohi yakin neman zabe, ko yin hi da tarurrukan / Haɗin gwiwar Masu ruwa da tsaki kamar yadda ya yi .
“Ba tare da la’akari da siyasarmu ba, ina yi wa kowa addu’a a wannan Disamba. Allah Madaukakin Sarki ya albarkace mu da yalwar arziki, ya kiyaye mu baki daya don ganin sabuwar shekara.” Inji shi
A wani labarin kuma, Gwamnoni Su Sakar Wa Kananan Hukumomi Kudaden Su– Gbenga Daniel Ya Goyi Bayan Buhari