Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta gayyaci Daraktan gammayyar kungiyar kare hakkin Dan Adam ta jihar Kano Karibu Yahaya Lawan Kabara ta (Global Community For Human Rights Network) bisa zargin kungiyarsa da siyar da wani fom ga al’umma da sauran zarge-zarge da ake yi masa.
Sashin binciken manyan laifuka na rundunar da ke Bamphai ne suka yi masa gayyatar a safiyar ranar Alhamis, wanda ya kuma amsa Kiran rundunar kuma ya ce ya ji dadin wannan zuwan da yayi.
A wani taron manema labarai da ya kira, a yammacin yau Alhamis Karibu Kabara ya ce cikin zargin da ake masa wanda yake zargin wani mutum ne ya kai tsogomin sa, da cewa yana siyar da wani from wanda ake ganin ya sabawa doka, ya ce yana cikin dokar kasa da kundin tsarin mulkin kungiyarsa na siyar da fom din kungiyar.
Ya ce dokar farko ta wannan kungiya ta bada damar siyar da fom kuma yana cigaba da siyar da wannan fom, “mun gabatar da takardar rijistar wannan kungiya ta CAC da duk abun da ‘yan sanda suka nema kuma sun tabbatar da ingancin su.
Kabara ya ce Mun barranta da duk wata kungiyar Human Right da take raji a Kano mutukar bata da rijistar CAC, domin idan bata da ita bata kan doka, ko wacce ce domin akwai wanda Muka ji labarin yana cewa Mu bamu da wannan rijista.
Ya kara da cewa yanzu abun kunya ne akansa, ya ishe shi da ya barranta kansa ko kuma Mu kai shi kara Kotu, domin bata mana suna da yayi ba daidai ba ne, kuma a fom din namu babu maganar daukar aiki ko biyan albashi ga mutum.