Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya yi ikirarin cewa gwamnati mai ci karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta gaji mataccen tattalin arziki daga tsohuwar gwamnatin ta.
DAILY POST ta tuna cewa ita ma gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi kukan cewa ta gaji tattalin arzikin da ya kusan durkushe daga gwamnatin Muhammadu Buhari da ta shude.
Karanta nanZaben Gwamnan Nasarawa: PDP ta Garzaya Kotun Koli Kan Hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta Yanke
Soludo, wanda ya yi magana irin wannan a ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politics Today, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnati mai ci.
Ya yi zargin cewa babban bankin Najeriya na buga kudi ba bisa ka’ida ba, wanda a cewarsa, ya taimaka wajen faduwar kudin kasar.
Tsohon gwamnan na CBN ya bayyana cewa, buga kudi ba bisa ka’ida ba, ya sabawa dokar 2007 da ke kula da babban bankin.
Ya danganta halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki a halin yanzu da irin rikon sakainar kashi da gwamnatin da ta gabata ta yi, yana mai bayyana tattalin arzikin da ta bari a matsayin mataccen doki.
Ya ce, “Mun zauna a nan kasar nan, muka ga hukumomin kudi suna buga kudi a zahiri.
A wani labarin kumaMuna Fatan Kotun Koli Za Tayi Mana Adalci-Gwamnonin PDP
Kuma don hana mu kaiwa ga inda muke a yau, shi ya sa muka samu wata magana karara wacce ta hana Babban Bankin bayar da lamuni da rikon sakainar kashi, inda ya ba gwamnatin tarayya hanyoyi.
Wannan gwamnati ta gaji tattalin arzikin da ya mutu ta mahangar tattalin arziki wannan gwamnati ta gaji mataccen doki da aka ga a tsaye amma mutane ba su san ya mutu ba. Ina ganin yana da mahimmanci ‘yan Najeriya su fahimci wannan.