Babban Bankin Najeriya CBN ya karyata wata sanarwa da aka yada a shafin Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari a shafin Instagram,Punch ta rawaito.
A cikin sanarwar da aka raba a shafin na Aisha Buhari a ranar Talatar nan, cewa tsofaffin Naira da suka hada da N500 da N1000 za su ci gaba da kasancewa a kan doka nan da kwanaki 70 masu zuwa, har zuwa 1 ga watan Mayu, 2023.
KU KARANTA: El-Rufai Ya Musanta Cewar Zai Rushe Wani Banki
Da yake karyata labarin, CBN ya sake fitar da wani sako, inda ya bayyana wanda Aisha ta yada a matsayin “labari na karya.”
Babban bankin na CBN ya ce, “domin kaucewa shakku, kuma bisa tsarin watsa shirye-shiryen shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu, 2023, an umurci CBN da sake fitar da tsoffin takardun kudi na Naira 200 kawai, kuma ana sa ran za a yi ta amfani da su a matsayin takardar kudi na doka har kwanaki 60, kwanaki har zuwa Afrilu 10, 2023.
“Don haka ya kamata jama’a su yi watsi da duk wani sako da/ko bayanan da Babban Bankin Najeriya bai fito a hukumance ba kan wannan batu.
Ana shawarci manema labarai da su tabbatar da duk wani bayani daga tushe kafin su wallafa.
A wani labarin kuma, Sambo, Makarfi, Yero sun sha alwashin kawar da APC a Kaduna
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi da Ramalan Yero, sun sha alwashin dawo da jam’iyyar PDP kan karagar mulki a jihar Kaduna.
Sun sha alwashin yin duk mai yiwuwa don ganin sun kawar da jam’iyyar All Progressives Congress, APC.