CBN ya yi karin haske kan karancin Naira
Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce isassun takardun kudi na Naira na yaduwa a yayin da ake samun rahotannin karancin kudaden.
A cikin wata sanarwa da Sashen Sadarwa na Kamfanin na CBN ya fitar, babban bankin ya bayyana dalilan da suka janyo karancin kudin Naira a wasu sassan kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN:Falana ya ba Tinubu mako biyu ya biya diyya ga wadanda harin jirgin sama ya rutsa da su
Matakin na CBN ya biyo bayan korafe-korafe da wasu abokan huldar bankuna ke yi kan karancin kudin da ake samu na Naira a kananun bankuna, da ATN, da wajen masu (PoS), da wajen masu canji.
Sai dai babban bankin ya ce ana ganin ana fama da karancin kudin ne sakamakon yadda bankuna ke cire kudade daga rassa daban-daban na CBN.
Ya bayyana cewa janye firgici da abokan cinikin banki ke yi shi ma wani bangare ne ya haddasa karancin.
Babban bankin na CBN ya ce babu karancin kudin Naira, yana mai cewa akwai wadatattun kudaden a tattalin arzikin kasar.
“An jawo hankalin CBN akan rahotannin da ake zargin ana fama da karancin kudi a bankuna, ATMs, PoS da BDC a wasu manyan biranen kasar nan.
“Binciken da muka yi ya nuna cewa ana ganin karancin kudi a wasu wuraren ya samo asali ne saboda yawan cire kudi daga rassan CBN da DMBs suka yi da kuma firgita da kwastomomin da ke cirewa daga na’urar ATM.
“Yayin da muke lura da damuwar ‘yan Najeriya game da samar da tsabar kudi don hada-hadar kudi, muna so mu tabbatar wa jama’a cewa akwai isassun takardun kudi na ayyukan tattalin arziki a kasar,” in ji sanarwar.
A wani labarin kuma:Yanzu Matasan Najeriya sun rungumi gwajin cutar Ƙanjamau – NIMR
Wani sabon bincike da aka gudanar a Najeriya ya nuna cewa yawan gwajin cutar kanjamau a tsakanin matasan Najeriya ya karu daga kashi 7 cikin 100 zuwa kashi 80 cikin 100 a cikin shekaru biyu ta hanyar amfani da kayan gwajin cutar kanjamau.
Masu binciken da suka gudanar da binciken a Cibiyar Nazarin Likitoci ta Najeriya, NIMR, tare da hadin gwiwar Jami’ar Washington da Jami’ar North Carolina, sun gano cewa kashi 20 cikin 100 na matasan Najeriya na amfani da kwayoyi a wani lokaci a rayuwarsu.