Babban Jami’in leken asirin Amurka, William Evavina ya zargi kasashen Chana da Rasha da kuma Iran da yunkurin yiwa shirin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba tuggu.
Sanarwar da Daraktan ya gabatar ta ce kasashen na yin amfani da matakai na boye da bayyane wajen dauke hankalin masu kada kuri’u a zaben mai zuwa.
Daraktan ya ce China ba ta bukatar ganin shugaba Donald Trump ya samu nasarar ci gaba da zama a karagar mulki, yayin da Rasha ke neman yiwa Joe Biden zagon kasa.
Jami’in ya ce bukatar Iran ita ce yin zagon kasa ga shirin baki daya da kuma rarraba kan al’ummar kasar wajen yada bayanan karya ta kafofin intanet.