Gwamnatin jihar Bauchi karkashi jagorancin Bala Muhammad ta sauke wasu sarakunan gargajiya 6 daga kan karagar mulkin su, Daily Trust ta rawaito.
Sanarwar tsige sarakunan gargajiya 6 ta fito ne ta hannun hukumar kula da kananan hukumomi ta jihar.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Wasu Makarantu Zuwa Naira ₦100k
Hakan ya biyo bayan samun su da “hannun a tsoma baki a harkokin siyasa na bangaranci da sauran munanan dabi’u”.
Sarakunan da abin ya shafa sun fito ne daga masarautar Bauchi da kuma masarautar Katagum.
Daukar matakin korar dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da rattaba hannun mukaddashin babban sakataren hukumar kula da kananan hukumomi Malam Nasiru Ibrahim a madadin shugaban hukumar da aka rabawa manema labarai a Bauchi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar kula da kananan hukumomi ta amince da korar wasu sarakunan gargajiya shida a masarautar Bauchi da masarautar Katagum.
“Hakan ya biyo bayan shigarsu cikin harkokin siyasa ta bangaranci, rashin da’a, kwace dazuzzuka ba bisa ka’ida ba, sare itatuwa, da almubazzaranci da dukiyar al’umma da rashin bin doka da oda wanda ya saba wa ka’idar aikin gwamnati.”
“Wadanda abin ya shafa a cewar sanarwar sun hada da;
Alhaji Aminu Muhammad Malami, Hakimin Udubo; Alhaji Bashir Kabir Umar Hakimin Azare, Umar Omar, Dagacin Kauyen Gadiya da kuma Umar Bani Dagacin Kauyen Tarmasawa dukkan su a masarautar Katagum.
“Wadanda aka kora daga masarautar Bauchi akwai Bello Suleman, Dagacin Kauyen Beni da Alhaji Yusuf Aliyu Badara Dagacin Kauyen Badara.”
“Don haka sanarwar ta umurci sarakunan gargajiyar da abin ya shafa da su mika wa sakatarorinsu da kuma majalisun masarautun su domin nada jami’an da za su sa ido har zuwa lokacin da hukumar za ta nada manyan sarakunan.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Wasu Shugabannin Makarantu 3 Kan Abu 1
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandire guda uku a jihar nan take saboda kin zuwa wurin aikinsu.
Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Ameen Yassar ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.