Cikin kashi da kwazazzabo muke kwana —– Daya daga cikin Daliban da aka sace
Wakilimu Shu,aibu Ibrahim Gusau
Bayan Sun koramu a kasa babu ko takalma cikin kashi da kwazazzabo muke kwana cikin tashin hankali.
Hakan ya fitone daga bakin daya daga cikin daliban da akayi garkuwa dasu a jihar zamfara, wanda suka sami kansu cikin daren litinin din nan wanda a halin yanzu suke gidan gwamnatin jihar zamfara.
Ta kara da cewa bayan an korasu babu takalma ga sanyi, duk da cewa sun ce ba, a barsu da yunwa ba suna basu abinci.
Sai dai wasu daga cikinsu sun sami raunuka a kafafunsu, inda tace wasu sun sami gwabcewa a kafafunsu, kamar yadda ta bayyana cewa ita kanta ta sami gwabcewa amma sune suka gyara mata kafa.
Daya daga cikin mahaifan yaran wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa yana cikin farin ciki sai dai kamar yadda yace yana bada sako ga wadannan barayin cewa suji tsoron Allah su sami sana’aryi wannan ba Sana’a bace.
A cikin darennan ne aka sako Daliban cikin mummunar yanayi, sai dai gwamnati ta samarwa kowace daga cikinsu an bata hijabi, don suturta Kansu, daliban da aka dauke a garin jangebe dake karamar hukumar Talatar mafara a jihar zamfara su kimanin 279, a halin da ake ciki yanzu suna cikin gidan gwamnatin jihar zamfara.