Cikin Shekaru 2, Najeriya ta samu mutane dubu 250,00 da suka kamu da cutar Covid-19, inda 3,000 suka mutu
Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Ƙasa NCDC, a cikin shekaru biyu ta samu mutane dubu 250,000, tare da mutuwar mutane 3,000 a Ƙasar.
Cibiyar a cikin jawabin data fitar, ta bayyana cewa, a wani ƙoƙari na inganta ɓangaren Lafiya, da kuma kula da manyan Cututtuka, da kuma bada gaggawa ga Cututtuka masu tasowa, Ƙasar nan dai ta ɗauki darasi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnonin APC Sun Gana Da Shugaba Buhari, Sun Ce Taron Jam’iyyar Ya Tsaya A Ranar 26 Ga Watan Maris
Ta bayyana cewar ranar 27 ga watan Fabrairu yayi dai-dai da ranar da Ƙasar ta cika shekaru biyu da cutar, inda a ranar ta gano mutum na farko da aka samu yana da cutar a Najeriya.
A cewar NCDC, cutar Covid-19 ta zamanto cuta da aka fuskanta a duniya, tana da kuma samfarin ta masu hatsari, duk da yanayin da take.
Sanarwar tayi dubi dacewar “wannan ya sanya mun koyi darasi daga wannan annoba na ɗaukar matakan gaggawa. Yanzu Dole mu tun kari ɓarkewar cutar Kwalara, da Zazzaɓin Lassa, daya haɗu da cutar Covid-19