- Jam’iyyar PDP ta dakatar da duk wasu daukar matakan ladabtar da ‘ya’yanta kan ayyukan da suka yi na kin jinin jam’iyyar a zaben daya gabata na 2023.
- Daukar matakin jam’iyyar wani ci gaba ne a kokarin da shugabannin jam’iyyar na kasa ke yi na sanya da’a tare da samun cikakken sulhu a jam’iyyar.
- Jam’iyyar tayi hakanne domin kafa wani kwamiti da zai duba duk wasu batutuwan da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi na rashin da’a da cin amanar jam’iyyar a zaben.
Jam’iyyar PDP ta dakatar da duk wasu daukar matakan ladabtar da ‘ya’yanta kan ayyukan da suka yi na kin jinin jam’iyyar a zaben 2023 da aka kammala,Tribune Online ta rawaito.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na kasa Debo Ologunagba ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa matakin na NWC wani ci gaba ne a kokarin da shugabannin jam’iyyar na kasa ke yi na sanya da’a tare da samun cikakken sulhu a jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dakyar Na Sha: Yadda Wasu Jiga-Jigan LP Suka Dauki Nauyin ‘Yan Daba A Kaina a Kotu – Apapa
Kwamitin gudanarwa na kasa na babbar jam’iyyar adawa ta kasa ta kuduri aniyar yin hakan ne a taronta na 571 a ranar Talatar da ta gabata, domin kafa wani kwamiti da zai duba duk wasu batutuwan da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi na rashin da’a da cin amanar jam’iyyar a zaben.
Ologunagba ya kara da cewa: “Wannan kudiri na NWC ya yi daidai da ikonta a karkashin sashe na 29 (2) (a) da (b) da sashe na 31 (2) (c), (d) da (i) na kundin tsarin mulkin PDP. (kamar yadda aka gyara a cikin shekarar 2017).
“Kazalika, NWC ta ba da umarnin cewa babu wata kungiyar jam’iyya a kowane mataki da za ta fara daukar duk wani mataki na ladabtarwa a kan kowane dan jam’iyyar ba tare da la’akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP (kamar yadda aka gyara a shekarar 2017) ba.
NWC ta bukaci daukacin mambobinta da su ci gaba da mai da hankali kan manufofin jam’iyyar “a matsayin kungiyar dimokuradiyya mai bin ka’idoji da tsarin mulkin mu yayin da muke samar da ci gaba tare da samar da dawwamammen sulhu, da’a da hadin kai a jam’iyyarmu.
A wani labarin kuma, Buhari Na Jimamin Mutuwar Jami’an Ofishin Jakadancin Amurika Da Wasu Mutane
Bayan wani hari da aka kai kan ayarin motocin ofishin jakadancin Amurka a jihar Anambra, a ranar Talata, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana alhininsa, tare da jajantawa iyalan wadanda aka kashe a lamarin.
Sakon ta’aziyyar Buhari na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, mai take, ‘Shugaba Buhari ya yi alhinin kashe jami’an ofishin jakadancin Amurka da ‘yan sanda da sauran su a jihohin Filato da Binuwai.