Rundunar sojin Najeriya ta ce ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan wani faifan bidiyo da ke nuna yadda jami’anta ke cin zarafin wani farar hula a wani otel da ke jihar Kaduna.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa A cikin faifan bidiyon, an ga wasu mutane sanye da kayan sojoji suna cin zarafin fararen hula.
Sai dai a wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ranar Lahadin nan, ya ce idan aka same su da laifi za a hukunta su kamar yadda dokar rundunar sojin ta tanada.
KARANTA WANNAN Yadda Wasu Sojoji Suka Lakadawa Jami’an Wata Hukuma Dukan Tsiya
A wani bangare sanarwar ta ce, “An kawowa rundunar sojin Najeriya wani faifan bidiyo na tsokana da rashin yarda da ke yawo a shafukan sada zumunta.
“Lamarin da aka yi Allah wadai da shi wanda aka ce ya faru ne a wani otal da ke wuraren shakatawa na 2Season, a Kaduna, cin zarafi ne ga da’a da kwarewa, jajircewa, sadaukar da kai da kuma hidima ga bil’adama da Sojoji ke wakilta.
“A matsayina na runduna mai da’a kuma mai bin doka da oda da ke tabbatar da martabar kundin tsarin mulkin kasa, kare kimar kasa da kuma ba da taimako ga hukumomin farar hula, rundunar sojin Najeriya ba ta da wani hannu a kan duk wani abu da ya saba wa hakkoki da walwalar ‘yan kasa.
“Saboda haka, hukumomin sojojin Najeriya sun ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan faifan bidiyon da aka gani don tabbatar da sahihancin sa, da nufin zakulo wadanda suka aikata laifin.
“Sakamakon bincike da kuma takunkumin da aka sanya wa mutanen da ke sanye da rigar soja, wadanda suka aikata munanan ayyukan, idan aka gano cewa jami’an sojojin Najeriya ne, za a byi musu daidai da tanadin dokar rundunar sojin.”
Jaridar Punch ta rawaito cewa Ya kuma bukaci duk ‘yan kasa masu bin doka da oda da su rika gudanar da sana’o’insu na halal ba tare da fargabar cin zarafi ko tsoratarwa daga kowane bangare ba, sannan su kai rahoto ga ofishin kare hakkin bil’adama na Sojojin Najeriya da ke shelkwatar sojojin Najeriya ko kuma dibishin na runduna.
A Wani Labarin Kuma FAAN Ta Gargadi Kungiyoyin Kwadago Na NLC, TUC Kan Wani Dalili
Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Kasa FAAN, ta bukaci kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC da su kaurace wa harkokin zirga-zirgar jiragen sama a filayen jiragen sama saboda korafin da suke yi a Owerri.
Hamisu Yadudu, Manajan Daraktan FAAN ne ya bayyana haka a Legas ranar Lahadin nan yayin da yake zantawa da manema labarai.